Daga Littafin Amanna (20) — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

Madubin Rayuwa

Daga Littafin Amanna (20)

Published

on


Jikin Khamis yana rawa ya tsaya daga nesa da Saloon din ya juyo ya dubi Iziddin ya ce “bari in shiga in kai mata kudin da zata biya, ka san Saloon din mata ne ba zasu so mu shiga ba mu maza shiyasa ma na tsaya daga nesa.”

Iziddin ya ce “toh, mu jira a gama mata mana sai mu dauke ta tunda ga dare zai yi, ita ba motar dawowa gare ta ba, ga motarka ta baci.”

Khamis ya zabura yana rawar jiki ya ce “ a a kada in bata maka lokaci rayukan matanka ya baci ai ni yanzu tsoron Nauwara nake ji gani take ni nake janka yawo gara in kai ka gida in damka ka a hannunsu in ya so in fito da motar in dawo in dauke ta bayan magriba.”

Iziddin ya yi murmushin karfin hali, ya ce “ba damuwa shiga ka fito.” Khamis ya fice da sauri yana laluba aljihu, bandir din kudi ne a aljihunsa naira dubu hamsin haka ya shiga ciki har a garin sauri wayarsa ta fado daga kan cinyarsa bai lura ba Iziddin na kallonsa, sai da ya shige Iziddin ya fito ya dauki wayar. Abin da ya fara budewa a jikin wayar sunan Sahiba 2 ya budo lambar yana ganin lambar ya shaida lambar Zahidah ce wacce Aljannah ta taba kiransa da ita daman ya haddace. Saboda sanyin da kafarsa ta yi sai da ya kusa faduwa kasa, ya yi sauri ya rike jikin mota. Ya zagaya ya koma ya zauna a mazauninsa ya ajiyewa Khamis wayar a gaban mota sannan ya kurawa wata dalleliyar mota ido a bakin saloon din, ko tantama babu motar Zahidah ce dan lambar motar ma sunanta ne ‘HIDAH 3’ aka rubuta.

Karewa ma sai ga Aljannah ta fito daga Saloon din an aiko ta ta dauko wani abu a cikin motar, ta matsa mukulli ta bude, ta dauko wata leda sannan ta mayar da kofar ta rufe. Iziddin ya fito daga mota da sauri ya tunkaro Aljanna yana yi mata dan kira. “Ke yarinya zo in tambaye ki.”

Ta daga ido a tsorace ta dube shi bata shaida shi ba sai ta dauke kai ta gaggauta runtumawa cikin shagon da sauri, sai abin ya bashi mamaki amma sai ya tuna ashe ba da wannan suffar ta san shi ba da suffar ‘yan caburos ta san shi, dan haka sai ya daina mamaki. Yana zaune a mota har yanzu dai khamis shiru sai da ya jima sosai ya fito da sauri dauke da wannan ledar da Aljanna ta dauko a mota.

Ya shigo a gigice yana laluba aljihu yana neman wayarsa sai gata a ajiye a gaban mota, ya yi ajiyar zuciya ya kalli Iziddin ya yi dariya ya ce “kaina fa ya dauki zafi ina ciki in ta neman waya ashe ma na barta a nan a ajiye.”

Iziddin ya yi murmushin karfin hali ya ce “sai a hankali abubuwan ne da yawa.”

Khamis ya wurga leda a kujerun baya ya ce “kayanta ta bani in kai mata gida wai gara ta dawo a motar haya.”

Iziddin ya tabe baki ya kalle shi da gefen ido ya yi shiru yana mamakin yadda Khamis ya zama mashahurin makaryaci kuma mayaudari, dan ada bai taba sanin ashe haka yake ba.

Su ka ci gaba da tafiya Khamis yana ta zuba masa karya shi kuma yana sauraronsa dan shi a yanzu babu abinda Khamis zai fada a duniya da zai yarda da shi.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!