‘Dalilin Da Ya Sa Buhari Ke Bukatar Wamakko A Yankin Sokoto’ — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

‘Dalilin Da Ya Sa Buhari Ke Bukatar Wamakko A Yankin Sokoto’

Published

on


Abin da sauran ‘yan siyasar Jihar Sokoto ba su gane game da sirrin nasarorin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ba shi ne kyautarsa da haba-habarsa da jama’a. Ba kamar sauran ‘yan siyasa ba, Wamakko bai da riko, bai da rowa, bai da jin izza, kazalika bai da kyamar zama da wadanda ya fi su kima da daraja nesa ba kusa ba.

Bahaushe yakan ce hali abokin tafiya. Nason da wadannan halaye suka yi a shaksiyyar Wamakko ya sa a ko’ina yake yana tare da dimbin jama’a ana hada-hada kamar kasuwa. Kuma hakan ne ya sa har yanzu yake jan zarensa a siyasar Jihar Sokoto.

Jaridar The Guardian ta ranar 5 ga Oktoba, 2018, ta ruwaito cewa: “Sanata Wamakko ya lashe zaben furamare na mazabar Sanata ta Sokoto ta Arewa a jam’iyyar APC ba tare da hamayya daga kowa ba.”

Ga jam’iyya mai farin jini irin APC, wacce kuma ke mulkin kasa, amma a ce babu dan hamayya a takarar sanatanta a yankin da ta fi tagomashi, hakan hujja ce da ke tabbatar da cewa, farin jinin Sanata Wamakko ba farin jini ne da ke daukar kishiya ba, zallan farin jini ne mara musharaka. Ba kuma komai ya sa hakan ba face nagartattun halayen can nasa.

Irin wannan mutumi ne Shugaba Muhammadu Buhari yake bukata a wannan lokaci da ake tunkarar zabe. Domin shi ne kadai zai iya kawo wa Buhari kuri’a ko da gwamnan jiha ba ya so. Alhamdulillahi kuma a ranar da ya sake lashe zaben furamare na sanata, a jawabin da ya gabatar, Sanata Wamakko ya ce, zai yi wa Buhari aiki domin tabbatar da Nijeriya ta gyaru bisa kyawawan manufofin shugaban kasa.

Idan da Buhari zai samu ire-iren Wamakko guda 40 a fadin Nijeriya, to, sai dai a ce ya je ya kwanta ya yi barci a zaben 2019. Saboda bai da abin fargaba.

Abdullahi Musa Makka, danjarida ne mai zaman kansa a Abuja

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!