Dan Majalisa Mai Wakiltar Birnin Kano Ya Samar Da Na’urar Lantarki Ga Dan’agundi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Dan Majalisa Mai Wakiltar Birnin Kano Ya Samar Da Na’urar Lantarki Ga Dan’agundi

Published

on


Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Birnin Kano.Alhaji Dkt.Abubakar Nuhu Danburam yace zai cigaba da shiga gaba da kuma bada tallafinsa akan duk wani abu dazai kawo cigaba ga al’ummar mazabarsa da kuma jahar kano gaba daya ta share musu hawayensu.Yana bayyana hakane kuwa bayan yabawa da al’ummar mazabar Dan’agundi sukayi bisa wucewa gaba da dan majalisar yayi na sama musu da daukar dawainiyar sanya musu sabuwar tiransifoma  da yayi dan amfanar wasu unguwannin mazabar.

Alhaji Dkt.Abubakar Nuhu Danburam yace samarda sabuwar tiransifomar ta biyo bayan koke da aka kawo masane na cewa tiransifomar ta lalace tab akin shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Birni.Alhaji Ahmad Sabo Dada da Malam Abdullahi Tela da Rabiu Khadi da Baba Dan,agundi da Aminu Justis ya tura dan a duba a gyara amma sai aka ga bazata gyaru ba sai dai a samarda wata sabuwa.

Yace kasancewar samarda sabuwa  sai dai a mataki biyu ko dai yasa a ayyukansa na mazabu ko kuma ya nemi kanfanin KEDCO da sune keda alhakin bada tiransifoma,dan haka ya rubuta takarda garesu a matsayinsa na dan majalisar tarayya ya isarda koke da bukatar al’ummarsa.Bayan aikewa da takardar kuma yayi bibiya akanta  ya kuma tuntubi shugaban KEDCO na Kano.Alhaji Jamilu Gwamna wanda a baya sun taba aiki tare a Bakin Inland kuma sakamakon anyi zaman mutuntaka dashi ya kuma taimaka akai.

Dan majalisar na tarayya yace shugaban na KEDCO ya hadashi da wani darakta a kanfanin mai suna Injiniya Debid  Omolaye da shine ke kulawa da raba tiransifomar kuma aka bi duk wata hanya ta ka’ida suka bada sabuwar tiransifoma ranar litinin da yamma kuma a lokacin a zaton washe gari za’a iya tafiya yajin aiki kuma in aka tafi daukar tiransifomar zai wuya,dan haka nan  da nan ya samarda kudi N120,000 akayi dawainiyar dauko tiransifomar da kawowa inda za’asa.

Dkt.Nuhu Abubakar Danburam yace koda akazo aikin sawa ya bada kudi da aka canja fala-falai aka cire na katako akasa na sumunti tare kuma da gina matakala na inda za’asa tiransifomar  domin anfanar al’ummar wanda suka dau lokaci suna cikin halin kunci na rashin samun wuta sanadiyyar rashin tiransifomar wanda wutarda akae samu tana taimakawa al’umma ba kawai wajen basu haske ba harma da cigaban tattalin arzikinsu.

Suma a nasu bangaren al’ummar mazabar Dan’agundi sun bayyana cigaba da bada goyon bayansu ga Dan majalisar na tarayya bisa kulawa da yake basu,kuma sun karyata wasu maganganu marasa tushe da ake yadawa na cewa wai dan majalisar jaha mai wakiltar yankinne ya samar,sunce wannan Magana batune marasa tushe sun san dai sun kai kokensu ga dan majalisar jaha amma ba wani dauki daya kawo,amma cikin gajeren lokaci daga kai kokensu ga  Alhaji Dkt.Abubakar Nuhu Danburam dan majalisarsu na tarayya aka kawo musu dauki aka share musu yaway

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!