Gwamnan Bauchi Ya Karbi Bakuncin Malaman Darikar Tijjaniyya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Gwamnan Bauchi Ya Karbi Bakuncin Malaman Darikar Tijjaniyya

Published

on


Gwamnan jihar Bauchi, Lauya Muhammad Abdullahi Abubakar ya shaida cewar a karkashin gwamnatinsa babu wani dan jihar Bauchi da ake nuna masa fifiko ko danne masa hakkinsa ta addini, yana mai shaida cewar a karkashin gwamnatinsa ya yi kokarin baiwa kowani bangare na addini hakkinsu domin a cewarsa ba ya nuna banbancin Akida ko fahimta a karkashin mulkinsa.

Gwamna, na jawabi ne sa’ilin da ya amshi bakwancin manyan Malaman Darika da suka fito daga kasashen Moroko, Aljeriya da Senegal hadi da sauransu, a karkashin jagorancin Khalifa a darikar Tijjaniyya, Sheikh Muhammadul Kabir, a gidan gwamnati ta Ramat House Bauchi.

Gwamnan yana mai shaida cewar a bisa hakan ne aka samu dauwamammiyar zaman lafiya wanda ke janyo ci gaba ta fuskoki daban-daban a jihar, yana mai shaida cewar babu wani dan jihar Bauchi da ake tauye masa hakkinsa ta fuskacin fahimtar Akidarsa.

Ta bakinsa; “Daga lokacin da wannan gwamnatin ta fara zuwa yanzu, dukkan wani musulmi da yake jihar Bauchi an nuna masa shi dan asalin jihar nan ne babu wani banbanci ko na Darika ko na wani akida daban,” A cewar shi

Tun da fari, da yake jawabi a madadin masu ziyarar, Sheikh Mahiy Nyass daga can kasar Senegal ya jinjina wa gwamnan jihar ta Bauchi a bisa salo da tsarin da yake tafiyar da gwamnatinsa a kai, inda kuma ya jinjina masa a bisa amsarsu hanu biyu-biyu da ya yi.

Sheikh Mahiy, ya kuma shaida cewar shugabanin Nijeriya suna gayar muhimmanta malaman addinin Islama, don haka ne ya shaida cewar ta irin wannan fuskar Nijeriya za ta samu ci gaba ta fuskoki daban-daban, hadi da samun nasarar gwamnati mai ci.

Ya shaida cewar a tarihince yake kan yadda shugabanin a Nijeriya suke kula da harkokin da ta shafi addini, sai ya nemi shugabanin da su daure a hakan, wajen girmama Malamai, waliyai da jikokin Annabi.

A lokacin da yake gabatar da manyan baki da kuma malaman addini, hadi da jikokin Manzon Allah wa gwamnan, Alhaji Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi ya shaida cewar babbar makasudin kacewar Malamai da jikokin Manzon, a jihar Bauchin shine don su jinjina hadi da gode wa Shaikh Dahiru Bauchi a bisa shiryawa da jagorantar gudanar da babban Maulidin Sheikh Ahmadu Tijjani wanda ya gudana a jihar Gombe.

Jikan Shehu Tijjani, Sheikh Muhammadul Kabir ya jagoranci yi wa jihar bauchi da kasar Nijeriya addu’a ta musamman na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!