Gwamnatin Yobe Ta Ba Da Tabbacin Inganta Jin Dadin Malaman Makarantu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Yobe Ta Ba Da Tabbacin Inganta Jin Dadin Malaman Makarantu

Published

on


Gwamnatin Jihar Yobe ta shelanta cewar, nan gaba kadan ne zata kara daukar malaman makarantu a kokarin da take yi na kara inganta harkokin koyo da koyarwa a Jihar.

Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam a jawabin da ya gabatar a wajen taron zabar sababbin shugabannin kungiyar malaman makarantu ta kasa NUT reshen Jihar da aka gudanar a babban zauren taron kungiyar ta NUT dake garin Damaturu.

Gwamnan wadda mai rike da shugaban ma’aikatan Jihar Alhaji Kachallah

  1. Jumbam ya wakilta, ya ce jihar na bukatar karin malamai saboda

yawaitar dalibai da karin makarantun da ake da su a Jihar.

Ya kuma bada tabbaci ga ‘yan kungiyar ta NUT cewar gwamnatin Jihar zata yi duk abin da zata iya na ganin cewar ta ci gaba da kara habaka jin dadin malaman Jihar.

Alhaji Ibrahim Gaidam ya kuma hori malaman makarantun da su dauki halayyar nan ta lalubo sababbin hanyoyin koyarwa na zamani don samar da ilimi mai inganci ga al’umma.

Gwamnan ya kuma nemi sababbin shugabannin na NUT da yi kokarin sauke nauyin da aka dora musu musamman don gani harkokin koyo da koyarwa ya inganta ta yadda mambobin kungiyar za su zama kwararru na gari.

Sababbin shugabannin da aka zaba don jan ragamar kungiyar ta NUT a Jihar sun hada da Ado Idrissa a matsayin shugaba sai Haruna Maiwaram a matsayin mukaddashinsa, ya yin da aka zabi Muhammad Babiye K. A matsayin maji mai tara kudi sai kuma Ali Modu Babbangida a matsayin odita mai binciken kudi da sauransu.

Nasa na amincewa  da kuma nuna godiyarsa da wannan zabe da aka masa sabon shugaban Ado Idrissa ya bada tabbaci ga mambobin kungiyar cewar, zai yi iya yinsa don ganin ya jagorancesu cikin adalci, kana ya roke su da suma su ba shi goyon baya don ganin ya gudanar da shugabancinsa  kamar yadda ya kamata.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!