Kabiru Balleria Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars Na Riko — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Kabiru Balleria Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars Na Riko

Published

on


Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta raba gari da mai horas da kungiyar wato Ibrahim A Musa, mahukuntan wannan kungiya sun dauki wannan mataki ne bayan mai horas war ya gaza sa Pillars din ta lashe gasar cin kofin Aiteo da mai horas war yakai kungiyar wasan karshe da sukai rashin nasara a hannun Enugu Rangers a watan da ya gabata.

A yanzu dai mahukuntan kungiyar ta Pillars sun nada tsohon dan wasan kungiyar kuma mataimakin kociyan kungiyar, Kabiru Balleria a matsayin sabon mai horas wa amma na rikon kwarya kafin sukawo sabon mai horas wa.

Kafin sallamar Ibrahim A musa kano Pillars suntafi hutun makonni guda biyu kuma a yau ne ‘yan wasan na Pillars zasu dawo daukan Atisaye amma da sabon mai horas warsu na rikon kwarya wato Balleria.

Shugaban gudanarwar kungiyar ta Kano Pillars, Alhaji Tukur Babangida ya bayyana farin cikinsa da matakin da hukumomin kungiyar suka dauka kuma ya bayyana cewa nan gaba kadan kungiyar zata dauki sabon mai koyarwa.

“Wannan mataki ne wanda muka dauka domin ganin kungiyar taci gaba daga matakin data kai zuwa na gaba kuma muna bawa magoya baya hakuri cewa nan gaba kadan komai zai tafi yadda suke bukata” in ji Tukur Babangidaa Mu Ba – Christiano Ronaldo

 

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!