Ko Ka San Kwallo Nawa Benzema Ya Ci A Madrid? — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Ko Ka San Kwallo Nawa Benzema Ya Ci A Madrid?

Published

on


Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Karim Benzema, ya bayyana farin cikinsa bisa kwallo ta 200 daya zura a kungiyar tun bayan daya koma kungiyar a shekara ta 2009 daga Lyon.

Benzema ya bayyana hakane a hirar da yayi da manema labarai bayan tashi daga wasan da kungiyarsa ta Real Madrid ta lallasa kungiyar Biktoria Plzen daci 5-0 a wasan cin kofin zakarun turai.

Dan wasan, dan asalin kasar Faransa ya bayyana cewa duk da haka yanason yaci gaba da zura kwallo a raga domin daman saboda haka kungiyar ta siyoshi kuma yana godiya bisa damar da suka bashi.

“Ina buga wasa ne domin in rubuta tarihin kaina da kaina a kwallon kafa ta hanyar zura kwallaye a raga da lashe kofuna duk da dai cewa ina fuskantar suka daga bangarori da daman a magoya baya da ‘yan adawa” in ji Benzema mai shekara 30 a duniya

Yaci gaba da cewa “Wani lokacin zanci kwallo wani lokacin kuma banaci kuma haka kwallon kafa take amma abinda yafi muhimmanci shine yakasance kungiyarka tana samun nasara kuma muna yin hakan”

A karshe yace yana fatan cigaba da tallafawa kungiyar wajen shawo kan matsalolin da suka addabesu a kwanan nan kuma zaici gaba da bada gudunmawa domin ganin kungiyar ta cika burinta na wannan shekarar.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!