Kwazon Farfesa Peng Li Yuan A Matsayin Jakadiyar Yaki Da Cutukan Kanjamau Da Tarin Fuka — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

BABBAN BANGO

Kwazon Farfesa Peng Li Yuan A Matsayin Jakadiyar Yaki Da Cutukan Kanjamau Da Tarin Fuka

Published

on


Cutar kanjamau ko Sida ko HIB/AIDs, cuta ce dake karya garkuwar jikin dan Adam, sannan kuma ta kan yadu daga wani zuwa wani ta hanyoyin jima’i ko jini. Cutar kanjamau cuta ce da ta ja hankalin al’ummomin duniya la’akari da yadda take yaduwa da kuma asarar rayuka da take haifarwa.

An yi kiyasin cewa, a shekarar 2016, mutane miliyan 36.7 ne ke dauke da cutar, wadda ta haifar da mutuwar mutane miliyan 1. Tun bayan gano cutar a shekarun 1980 zuwa shekarar 2017, ta yi sanadin mutuwar mutane miliyan 35 a fadin duniya.

Cutar kanjamau na da mummunan tasiri kan al’umma, a matsayinta na cuta sanann kuma wadda take haifar da tsangwama. Cutar ta jawo hankalin al’ummomin kasa da kasa, sannan ta lakume makudan kudaden tun bayan da aka ganota a shekarun 1980. Yayin da kasashen duniya suka dukufa wajen ganin an kawo karshenta ya zuwa shekarar 2030 kamar yadda muradun ci gaba masu dorewa na MDD (SDG’s) suka tanada, kasar Sin ma ba a bar ta a baya ba, wajen cimma kokarin wannan muradi. Rahotanni na cewa, cikin shekaru 20 da suka gabata, kasar Sin ta taka rawar gani wajen rage yaduwar cutar da kuma inganta kiwon lafiyar wadanda suke dauke da ita. A yanzu, gwamnatin kasar ce ke samar da mafi yawan kudaden da ake bukata na gudanar da shirye shiryen yaki da cutar. Don ko a shekarar 2015, ana samun kimanin kaso 99 na kudaden da ake kashewa wajen yaki da cutar ne a cikin gidan kasar, wato daga gwamnati da kungiyoyin al’umma da bangarori masu zaman kansu. Haka zalika, daidaikun mutane ma ba a bar su a baya ba wajen gudanar da shirye-shiryen wayar da kai don yaki da cutar.

La’akari da irin kokari da jajircewarta ga harkar wayar da kai da yaki da cutar kanjamau ne Farfesa Peng Liyuan, uwargidan Shugaban kasar Sin Di Jinping, ta zama jakadiyar takaita yaduwar cutar na ma’aikatar lafiya ta kasar a shekarar 2006. A kuma watan Maris din shekarar 2007 ne ta zama jakadiyar takaitawa yaduwa da yaki da cutukan tarin fuka da kanjamau ta kasar baki dayanta. Har ila yau, a watan Junairun shekarar 2011 Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sanar da nada Farfesa Peng Liyuan a matsayin jakadiyar hukumar ta yaki da cutar Kanjamau da kuma tarin fuka.

A cewar Darakta Janar ta Hukumar a wancan lokaci Margaret Chan, hukumar WHO na da muhimman matakai da dabaru da kuma burin cimma yaki da tarin fuka da kanjamu. Ta ce cutukan biyu masu kisa, na sanadin rayuka sama da miliyan 3.5 duk shekara, galibi a kasashe masu tasowa. Wannan na haifar da dimbin wahalhalu da karin ayyukan kiwon lafiya tare da yin mummunan tasiri kan al’ummomi da tattalin arziki. Ta ce abun takaicin shi ne, yadda cutukan nan biyu ke tafiya kafada-da-kafada, inda daya ke tasiri kan daya. Sai dai cikin gomman shekarun da suka gabata, an samu nasara a yaki da cutukan, domin an san yadda za a dauki matakan kariya da kuma kula da wadanda suka kamu. Margaret Chan ta kara da cewa, duk da nasarorin, har yanzu adadin wadanda suke kamuwa da mutuwa sanadiyyarsu na da yawa. Ta ce Cutukan biyu na da hallaya iri guda, da mutane masu fada aji za su iya yin tasiri a yaki da su. Wato masu fama da cutukan nan biyu kan fuskanci tsangwama, wanda fitattun mutane za su iya bada gudumuwarsu na ganin an kawar da ita a tsakanin al’umma.

La’akari da matsayinta na Mawakiya kuma Tauraruwa dake da masoya a kasar Sin da ma kasa da kasa, da kuma aikin yaki da cutukan da ta dade ta na yi, hukumar WHO ta zabe ta a matsayin Jakadiyarta na yaki da cutukan biyu.

Farfesa Peng Liyuan, ta dade ta na fafutukar yaki da yaduwar cutukan nan biyu, inda aikin da take yi ya hada da kula da marayun da iyayensu suka mutu sanadiyyar cutar kanjamau, da bayyana muhimmanci gwajin cutar da kuma daukar matakan kariya. Jajircewa irin nata ne, ya sa ta je yankunan dake fama da talauci don ziyartar masu wadannan cutuka. Ta kan kuma bada gudunmuwa ga yaran dake fama da cutar kanjamau. sannan a matsayinta na tauraruwa, ta jajirce wajen yaki da tsangawamar da ake yi wa masu cutar kanjamau.

Ko a watan Junairun bana, hukumar yaki da cutar kanjamau ta MDD UNAIDS, ta karrama Farfesa Peng Liyuan, la’akari da irin rawar da ta taka da kuma gudunmuwar da ta bayar ga yaki da cutar kanjamau a duniya. Karkashin ayyukanta, an samu gagarumar nasara ta fuskar yaki da tsangwamar masu cutar kanjamau, inda mutane masu cutar ke samun hidimomin da suke bukata sosai fiye da baya, haka zalika ta kara fahimtar da mutane yadda za su taimakawa yara da matasa musammam ma yara marayu masu cutar, ta yadda za su rayu cikin koshin lafiya da martaba ba tare da tsangwama ba.

Da yake mika mata lambar yabon a wani biki da hukumomin UNAIDS da WHO suka shirya a Geneba na Switzerland, Daraktan Zartarwa na UNAIDS Micheal Sidibe, ya ce Farfesa Peng, ta taimaka sosai wajen wayar da kai game da cutar kanjamau a kasar Sin, wanda ya haifar da kauna da tausayawa masu dauke da cutar. Ya ce ta kasance bango ga masu rauni, musamman yaran dake da cutar kanjamau, kuma ta taimaka wajen samarwa yara muhalli ba kadai na rayuwa ba, har ma da samun ci gaba.

Ya ce aikin Farfesa Peng da sauran fitattun mutane masu fafatukar yaki da cutar Kanjamau, ya bada gagarumar gudunmuwa ga inganta kare yaduwar cutar daga uwa zuwa da a fadin duniya. Haka zalika, yunkurinsu ya sa yara dake dauke da cutar, na samun kulawa. A shekarar 2005, kasa da kaso 10 na yara masu cutar ne ke samun magani, amma karuwar gangamin wayar da kai da samar da magunguna, ya sa kusan kaso 50 na yara miliyan 1.8 dake fama da cutar a 2015 na samun magani.

Idan muka yi waiwaye, a shekarar 2015, Farfesa Peng Liyuan, ta yi hadin gwiwa da kungiyar matan shugabannnin kasashen Afrika kan yaki da cutar kanjamau a birnin Johannesburg na Afrika ta kudu, yayin taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC. Inda suka tattauna kan muhimman batutuwan da za su kai ga kawo karshen cutar ya zuwa 2030. Ta ce Kasar Sin za ta taimakawa kasashen Afrika yaki da cutar kanjamau, haka kuma za ta mara baya ga shirye-shiryen Hukumar WHO da ta UNAIDS na yaki da cutar a Afrika. Bugu da kari, za ta taimakawa shirye-shiryen nahiyar na samar da asibitoci da inganta kiwon lafiyar mata da yara. Har ila yau, ta yi kira da a kara kaimi wajen samarwa masu cutar magani tare da kaddamar da shirye- shiryen wayar da kai ta kafofin yada labarai domin kara fadakar da yara hanyoyin kariya daga cutar.

Yayin taron FOCAC na baya-bayan ma da aka yi cikin watan Satumba a birnin Beijing, Farfesa Feng, tare da matan shugabannin kasashen Afrika 37, sun kara haduwa, inda suka kaddamar da wani sabon shirin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika, domin kawo karshen cutar Kanjamau.

Da take bitar ayyukanta a matsayin jakadiyar yaki da cutar kanjamau da tarin Fuka ta duniya, Farfesa Peng Liyuan, ta ce hada hannu domin yaki da cutar kanjamau, matsaya ce guda da kasashen duniya suka cimma, kuma hadin gwiwar Sin da Afrika a wannan fannin ya na da inganci.

Ta ce taron na FOCAC ya samar da sabbin damarmakin zurfafa hadin gwiwar Sin da Afrika a fannin takaita yaduwar cutar kanjamau. Ta kara da cewa, a badi wato 2019, Kasar da kasashen Afrika da sauran hukumomin kasa da kasa masu ruwa da tsaki kan batun, za su fara aiwatar da wani shiri na shekaru 3,wanda ke da nufin kare kamuwar cutar tsakanin matasa da kuma inganta ayyukan kiwon lafiya a cikin al’umma.

Ita ma da ta ke tsokaci a matsayinta na jakadiyar yaki da cutar kanjamau ta hukumar raya kasashe ta Amurka wato USAIDS, Uwargidan shugaban Nijeriya Hajiya Aisha Buhari, ta ce la’akari da matsayinsu a cikin al’umma, su na da karfin fada a ji, shi yasa ma yayin taron na su na matan shugabannin kasashen Afrika da uwargida Peng na wannan karon, suka kara cin alwashin hadin gwiwa don yaki da cutar kanjamau. Kuma daga cikin abubuwan da za su yi, har da bin makarantu suna fadarkar da yara illolin cutar da matakan kariya da kuma kara kula da masu dauke da ita. Ta ce ita a nata bangaren ta bada shawarar a zage damtse wajen ilmantar da yara masu tasowa game da cutar, duba da yadda matasa suka fi yawa cikin wadanda ke dauke da ita.

Yayin taron, Darakta Janar na hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus da Daraktan Zartawa na shirin yaki da cutar kanjamau na MDD Michel Sidibe, sun bayyana tasirin da hadin gwiwar Sin da Afrika ta yi ga yaki da cutar, inda kuma suka yaba da namijin kokari da gudunmuwar da Farfesa Peng Liyuan ta yi wajen kara wayar da kai game da hanyoyin kariya da kuma kula masu cutar.

Kasar Sin ta dade ta na taimakawa nahiyar Afrika a yakin da ake da cutar kanjamau, inda ta tura jami’an kiwon lafiya zuwa sama da kasashen nahiyar 40 tare da samar da magunguna kyauta.

Micheal Sidibe, ya ce kasashen duniya sun samu gagarumar nasara a yaki da cutar kanjamau, amma kuma har yanzu da sauran rina a kaba, a don haka ake bukatar mutane irinsu Farfesa Peng Liyuan, da su ci gaba da wayar da kai da jagorantar kawo karshen cutar kanjamau da tarin fuka.

Hada karfi da karfe da aka yi a kasar Sin wajen yaki da cutar kanjamau, wanda ya hada da shigar gwamnati da kungiyoyin al’umma da bangarori masu zaman kansu da daidaikun mutane, ka iya zama muhimmin darasi ga sauran kasashen duniya. (Ma rubuciya: Fa’iza Mustapha, ma’aikaciyar sashen Hausa ta CRI)

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!