Rasuwar Sarkin Nasarawa: An Samu Gibi Mai Wuyar Cikewa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Rasuwar Sarkin Nasarawa: An Samu Gibi Mai Wuyar Cikewa

Published

on


 

  • Ya Yi Kokarin Tabbatar Da Zaman Lafiya – Gwamna Al-Makura
  • Rasuwarsa Babban Rashi Ne Ga Al’umma – Shugaban Majalisar Nasarawa

‘Ya Samar Da Hadin Kai da Kaunar Juna’

A jiya Alhamis ce mai magana da yawun kwamishinan ma’aikarar masautu da kananan hukumomi Ibrahim Adamu Shigafarta, ya  sanar da rasuwar Sarkin Nasarawa Alhaji Hasan Abubakar sakamakon gajeriyar rashin lafiya wadda ya yi jinya a Babban Asibitin kasa da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.

Kafin rasuwarsa shi ne sarki na 11 a jerin sarakunan masarautar Nsarawa. Marigayi Alhaji Hasan Abubakar ya rasu yana da shekara  79,  ya bar mata biyu  da ‘ya’ya 13, maza 8 mata 5. Marigayin Alhaji Hasan Abubakar ya zama Sarki a Masarautar Nasarawa da ke karamar hukumar Nasarawa a shekarar 2004, Ya kwashe  shekara 14 bisa karagar mulkin a masarautar Nasarawa.

Marigayi  Sarki Hasan Abubakar ya kasance mai kyawawan ayyukan ga al’ummar Masarautarsa. A lokacinsa, yankin Nasarawa ya samu ci gaba wajen tabbatar da zaman lafiya da kaunar juna a dukkan fadin masarautar ta Nasarawa.

Gwamanan jihar Nasarawa tare da Sarakunan jihar da manyan Sarakuna daga wasu jihohin ne suka samu halartar jana’izarsa wadda aka gabatar a Fadar Nasarawa sanna kuma aka binne shi a Fadarsa da ke garin  Nasarawa kamar yadda Musulunci ya tanada.

Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura, ya bayyana Marigayi sarkin Nasarawar, Alhaji Hassan Ahmed II mni, MFR, a matsayin shugaban da ya samu nasarar tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’ummar masarautarsa da na jihar Nasarawa da ma na kasa ba ki daya. Haka kuma ya ci gaba da cewa, aba al’ummar jihar Nasarawa kawai ne suka yi wannan rashi ba, rashin ya shafi al’ummar kasa ne baki daya Al-makuran ya bayyana hakan ne jim kadan da kammala jana’izar ta sa.

Ita ma a nata nuna alhinin majalisar dokokin jihar ta bayyana rasuwar Sarkin a matsayin wani babban gibi da zai wuyar cike wa. Jawabin hakan ya fito ne ta bakinsakataren yada labaran shugaban majalisar Jibrin Gwamna, a garin lafiya.

Shi kuwa shugaban majalisar  Alhaji Ibrahim Abdullahi,ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin babban abin da ya girgiza jama’a na ciki da wajen jihar.

Ya ci gaba da cewa Marigayin ya samar da kyakkyawan yanayin da aka samu fahimtar juna wanda kuma hakan ta tabbatar da zaman lafiya a jihar Nasarawa baki daya.

Sarkin Nasarawa mutum ne mai kaunar zaman lafiya da karfafa dakon zumnci a tsakanin al’umma

Tarihinsa ya nuna cewa, bayan Marigayi Sarkin Nasarawa, ya sami nasarar saukan Karatun Alkur’ni Mai Girma a garin na Nasarawa, sai ya fara karatun Boko a shekarar 1945, inda ba tare da bata lokaci ba ya sami cin jarabawar shiga Makarantar gaba da Firamare ta, ‘Katsina-Ala Middle School a shekarar 1949.

A nan din ma ya cinye jarabawar na shi a wannan makaranta ta, Katsina-Ala Middle School, sai ya sami shiga Kwalejin horas da Malamai ta Bauci, a shekarar 1954, ya kuma kammala makarantar ne a shekarar 1956. Ya kasance a Kwalejin ilimin kimiyya na karkara, da ke Minna, daga shekarar 1958-1959, Babban Kwalejin horas da Malamai ta Ilorin, ‘Higher Teachers Training College,  Ilorin, daga Shekarar 1980-1982; Cibiyar Horas da manyan ma’aikata ta Kaduna, ‘Staff Debelopment Centre, Kaduna, a shekarar 1982; Cibiyar gudanar da harkokin mulki ta Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, ‘Institute of Administration, ABU, Zaria, a shekarar, 1984 da kuma, ‘ Institute of Public Administration Management, daga shekarar 1982-1983.

Alhaji Hassan Ahmed II, yana daga cikin mahalarta Cibiyar koyar da dubarun mulki da siyasa ta, Kuru, kashi na farko, “National Institute for Policy and Strategic Studies, Kuru,” daga shekarar 1979-1980. Kwas mai lamba 01.

Marigayi Sarkin na Nasarawa, ya fara aiki ne a matsayin Shugaban Malamai a babban Makarantar Firamare ta Nasarawa, daga shekarar 1960-1962, ya kuma yi aiki a dukkanin matakai uku na gwamnati, na kananan hukumomi, Jiha da gwamnatin tarayya. Ya rike mukamin Mataimakin babban Jami’in gudanarwa na Kaduna, 1963-1964, babban jami’in ilimi a Yola, babban jami’in gudanarwa a hukumar wasanni ta Jos, a tsohon lardin Binuwe da Filato, babban jami’i mai kula da Ofishin Jihar Filato, da ke Legas, Sakatare a kananan hukumomin, Mangu da Jos, Babban Sakataren Gwamnan mulkin Soja na Jihar Filato,  Kwamishinan harkokin cikin gida na Jihar Filato, Mataimakin babban Sakatare a ofishin Gwamnan mulkin Soja na Jihar Filato daga shekarar, 1979-1980. Hakanan shi ne Sakatare kuma Darakta a gwamnatin, ya yi shekaru 11 a cibiyar koyar da harkokin siyasa da masana’antu, (ITF), wanda hakan ya sanya ya zama shugaban cibiyar da ya fi kowa dadewa a shugabancin cibiyar ta ITF.

Bayan da ya yi ritaya daga aiki ne, Marigayi Alhaji Hassan Ahmed II, ya riki mukamin shugaban kula da harkokin ma’aikata ta Jihar Nasarawa, da kuma shugaban hukumar gudanarwa ta Kwalejin Ilimi da ke Akwanga.

Alhaji Hassan Ahmed II, ya sami lambobin yabo masu yawa daga cibiyoyi daban-daban, da suka hada da lambar yabo ta ma’aikata masu kwazo a shekarar 1995, wanda Marigayi Shugaban gwamnatin mulkin Soja na wancan lokacin Janar Sani Abacha, ya ba shi, da lambobin yabo na kasa masu yawa, da suka hada da, (Member of the Order of the Federal Republic of Nigeria) (MFR), wanda tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ya ba shi a shekarar 2001. Abubuwan da ya fi sha’awa sun hada da Karance-karance, hawan doki, ninkaya da tafiye-tafiye. Ya ziyarci kasashe masu yawa a yammacin Turai, arewaci da kudancin Amerika, Japan, Indiya, Saudi Arabiya, Hong Kong da kasashe masu yawa a arewaci, gabashi, kudanci, yammacin da tsakiyar Afrika.

Tuni dai akayi jana’izar marigayin a garin na Nasarawa, kamar yanda Addinin Musulunci ya tanada.

Gwamna Tanko Al-makura na Jihar ta Nasarawa, wakilan majalisar gudanarwa na gwamnatin Jihar, Sarakunan gargajiya, daga ciki da wajen Jihar da suka hada da Sarakunan Wase, Kanam da wasu manyan kasar nan duk sun sami halartar Jana’izan.

A daya daga cikin tattaunawar da ya yi da manema labarai, Sarkin yana cewa, “Bari na gaya maku, mafi mahimmancin abin da muke yi shi ne addu’a, a kowane lokaci domin samar da zaman lafiya, muna kuma ganin sakamakon addu’o’in da muke yi. Duk rigingimu da fituntunun da suke faruwa ba su iso mana nan ba sam. Muna cikin zaman lafiya, duk da halin kunci da wahalan da al’umman mu suke fama da shi. Za ka iya yin maganan zaman lafiya, amma ba wani ci gaba mai ma’ana da za a samu face an inganta sha’anin rayuwar al’umman mu. Kamar yanda na fada ne tun da farko, muna yi wa Allah godiya da Ya samar mana da zaman lafiya, sam ba mu da wata matsala.

“A matsayina na Basarake abin alfahari ne. mu a nan mutananmu suna girmama al’adun su, kamar maganan Sarauta, abu ne da ya kebantu ga iyalan gidan Hasan. In dai daga gidan ka fito, to kana cikin magadan wannan gadon Sarautar, ina mai farin cikin gadar magabatanmu. Ni din ne dai, rayuta ta ba ta canza ba, ina girmama ra’ayin al’umma ta. Don haka ina jin dadin kasancewa ta a matsayin ma’aikacin gwamnati sannan kuma Sarki Mai daraja ta daya. Na fahimci cewa jagoranci mahimmin abu ne, jagoranci shi ne, ka zauna da mutane kuma ka saurari mutanan, ka warware masu matsalolin su,” in ji Marigayi Sarkin Nasarawa, Alhaji Hassan Ahmed II

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!