Sama Da Lauyoyi 100 Za Su Kare Wadanda Ake Zargi Da Kisan Janar Alkali — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Sama Da Lauyoyi 100 Za Su Kare Wadanda Ake Zargi Da Kisan Janar Alkali

Published

on


Sama da Lauyoyi 120 ne da suka hada da manyan Lauyoyi masu mukamin SAN, suka nuna aniyarsu ta kare mutane 19 da aka kama a bisa zargin su da kashe tsohon babban jami’in rundunar Sojin Nijeriya mai kula da sashen gudanarwa na rundunar, Janar Mohammed Alkali.

Labarin hakan ya bayyana ne a lokacin da wadanda ake zargin suka rubuta wa mai shari’a Daniel Longji, na babbar kotun Jihar Filato, takardar neman beli a ranar Laraba.

Lauyan da yake kare wadanda ake tuhuman, Gyang Zi, ne ya shaida wa manema labarai cewa ya gabatar da takardar neman belin ne a bisa yarjejeniyar da aka yi tun da farko, inda ake tuhumar mutanan da aikata laifuka biyu, wadanda kuma suka musanta aikata laifukan.

Gyang Zi ya ce, “Sama da Lauyoyi 120 ne suke son shiga cikin tawagar Lauyoyin da za su kare wadanda ake tuhuman. Amma dai har ya zuwa lokacin ba a bayar da belin mutanan ba tukunna, amma dai yanzun ne muka rubuta bukatar neman belin. Duk mutanan da ake tuhuman sun musanta aikata laifin da ake tuhumar na su da aiakatawa Kakakin rundunar ‘Yan sanda na Jihar Filato, Matthias Tyopeb, ya shaida wa wakilinmu cewa, an gurfanar da mutanan da ake tuhuman ne a bisa hada baki da kuma aikata kisan kai.

Ya ce, “Ana tuhumar su ne da aikata laifuka biyu, hada baki a aikata laifi, a karkashin sashe na 97 da kuma aikata kisan kai a karkashin sashe na 221 na kundin dokokin Fenal Kod, na arewacin Nijeriya, wanda kuma ake aiki da shi a Jihar ta Filato. Duk an karanta masu laifin da ake tuhuman na su da aikatawa, sun kuma musanta aikata laifin. An daga shari’ar zuwa ranar 10 ga watan Disamba, domin a saurari bukatar neman beli. Ana tsare da wadanda ake tuhuman ne a gidan Yarin Jos.”

An ce, Janar Alkali ya yi ritaya ne daga aikin na Soja makwanni kadan da suka shige, kafin a shelanta bacewarsa a ranar 3 ga watan Satumba, kwana guda da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kauyan Dura-Du, da ke karamar hukumar Jos ta kudu, suka kashe akalla mutane 13.

An tsamo motoci uku daga wani tsohon kududdufin masu hakan kuza a garin na Duru-Du, a lokacin da Sojoji suke bincike, wanda Kwamandan runduna ta uku ta Barikin Rukuba, da ke Jos, Birgediya Janar Umar Muhammad, ya jagoranta.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!