Shugaba Buhari Ya Sa Dokar Ta-baci A Sashen Ruwa Da Tsaftar Muhalli — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Shugaba Buhari Ya Sa Dokar Ta-baci A Sashen Ruwa Da Tsaftar Muhalli

Published

on


Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya saka dokar ta-bacia kan samar da ruwan sha, tsafta da gyara muhalli a fadin kasar nan.

Shugaban ya sanar da hakan ne a ranar Alhalis ta jiya.

Bayanin hakan yana kunshe ne a cikin sanarwar da Mai bashi shawara ta musamman a harkar yada labarai Mista Femi Adesina ya raba wa manema labarai.

Shugaban ya ayyana hakan ne a lokacin da ya kaddamar da shirin sake gyaran ruwan na kasa da aka gudanar a fadarsa da ke garin Abuja.

A cewarsa, kafa dokar ta-bacin ta zamo wajibi, musamman saboda yawan karancin ruwan sha da kuma rage yawan cututtukan da ke a cikin ruwan sha a daukacin fadin kasar nan.

Shugaban ya ci gaba da cewa, matsalar ta karancin ruwan sha ta janyo yawan mutuwar al’umma a kasar nan. Shugaba Buhari ya shedawa wadanda suka halarci taron kaddamarwar cewar, yana sane Nijeriya ba ta samu cimma muradun karni na MDG na a fannin samar da tsaftatattacen ruwan sha da tsafta ba har shekarar da aka tsara shirin ta shige.

A cewar sa, shirin na muradun karnin, an so ne a cimma burin kashi 6.1 da kuma 6.2, amma a zahiri bukatun ya wuce hakan inda ya yi nuni da cewar, ba za a iya cin nasara a hakan ba in har aka ci gaba da tafiya a yadda ake yi a baya.

Shugaban ya sanar da cewa, “a saboda hakan ne ya sanya na goyi bayan wannan matakin na gaggawa a taron gaggawa da aka gudanar na majalisar kasa a cikin watan Afurilu wannan shekarar a fannin na samar da ingantacce ruwan shan.

Ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihihin da ke kasar nan, su ma su mar w a gwamnatin baya wajen cimma burin na samar da ingantaccen ruwa a jahohin su don a cimma burin samar da ingantaccen ruwan sha a shekarar 2030 mai zuwa.

Shugaban ya kuma umarci daukacin matakan gwamnati da ke kasar nan su kara zage damtse wajen yin aiki don ganin an cimma bukatar da ake da ita na samar da ingantaccen ruwan sha da bukatun tsafta a kasar baki daya.

Ya bayyana bacin ransa karara, a kan samun kididdigar da ke nuna karin samun yin bahaya a ko ina, da lacewar bututun tura ruwan sha a kasar nan.

Ya sanar da cewar, daga yanzu Gwamnatin Tararrya za ta tallafawa gwmnatocin jihohi a kan yadda su ma suka mayar da hankali wajen wanzar da shirin na WASH a jihohin su da kuma kawo karshen yin bahaya a ko ina a kasar nan baki daya nan da shekarar 2025.

Ya sanar da cawa, shirin samar da ruwan sha na kashi 32 bisa dari na shekarar 1990 ya yi kasa da kashi 7 bisa dari a shekarar 2015. Shugaban ya yi nuni da cewa, “kasar mu yanzu ta kai ta biyu a duniya wajen yin bahaya a ko ina da kimanin kashi 25 bisa dari na yawan al’ummar da muke da ita a kasar nan”.

A karshe Shugaban ya sanar da cewa, shirin WASH a karkara ba iya aiwatar da shi yadda ya kamata ba ganin cewar kashi 46 bisa dari na shirin ba’a ci wata nasar da ta kamata ba kuma kudin da aka zuba sun sauka da kashi 0.70 bisa dari na ma’aunin hadahadar tattalin arziki na GDP a shekarar 1990 zuwa kimanin kashi 0.27 bisa dari a shekarar 2015 wanda yake nuna ya yi kasa sosai, ya yi kasa da kashi 0.70 bisa dari a yankin Afirka ta Yamma.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!