Connect with us

MANYAN LABARAI

Bincike A Tashar Jirgi: Dole A Nemi Gafarar Atiku –Shehu Sani

Published

on

Dan majaliusar Dattijai mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gagauta neman gafarar dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Alhaji Atiku Abubakar, ba tare da bata lokaci ba.
LEADERSHIP A Yau ta ruwaito cewa, Atiku ya koka a kan yadda jami’an tsaro suka yi masa tare da ‘yan tawagarsa binciken kwakwaf a lokacin day a dawo daga kasar Dubai ranar Lahadi.
Shehu Sani ya yi tir da halayyar jami’an tsaron yana mai cewa, wannna kusan rashin iya aiki ne gaba daya.
Sanatan ya yi wadanna bayanan ne a shafinsa na Twiter, inda ya kara da cewa, “Aikin wuce gonad a iri da jami’an tsaron suka yi a kan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku abin a nyi tir da shi ne, wannan kuma wani abu ne da ba a taba gani ba a tarihin kasar. “Dole gwamnatin tarayya ta nemi gafarar wannna aiki da ta tabka da suna aikin da aka saba gabatarwa..”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!