Connect with us

LABARAI

Buhari A Paris: Barazanar Kurkuku Ba Ta Hana Sata A Nijeriya

Published

on

A ranar Lahadi ne Shugaba Buhari ya bayyana cewa, aikata laifukan satan dukiyar kasa sun shahara aNijeriya ta yanda dauri ba ya hana barayin aikata satan
Shugaban ya fadi hakan ne a birnin Paris, lokacin da yake gabatar da jawabi a kan illar satar dukiyar al’umma a wani taro da aka gabatar kan hakan a babban birnin na kasar Faransa.
A cewar sa, hanyar da ta fi dacewa da za ta tsoratar da masu aikata satan ita ce, a kwace duk wata dukiya da ta haihu daga dukiyar da aka sata din, a mayar da ita cikin baitul-malin al’umma.
Shugaban ya ce, “Ina farin cikin kasancewa daga cikin mahalarta kaddamar da wannan kungiya ta, Paris Forum, ina kuma son na yaba wa gwamnatin Faransa a kan wannan aikin da ta yi abin yabawa.
“Muna kuma yin godiya ga kasar Faransa da ta gayyaci Nijeiya cikin wannan kungiyar wacce ake bikin karni na kwance damara. Duk da cewa Nijeriya ba ta sami ‘yanci ba a wancan lokacin, sai dai ta taimaka wajen cimma sasantawan.
“Nijeriya ta taimaka da dakaru da wasu taimakon a wajen yakin a karkashin rundunar nan ta, Royal West African Frontier Forces.
“A wannan ranar tunawan, ina jinjina ga sadaukarwar duk wadanda suka kwanta dama a cikin wannan yakin da kuma wadanda suka jikkata a cikin sa.
“Sama da dakaru rabin milyan ne daga nahiyar Afrika suka shiga cikin mayakan kasar Faransa kadai. Hakanan an yi kwami sosai a gabashi da kudancin Afrika da sassan Kamaru da Nijeriya. Ba za mu manta da wannan ba,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!