Connect with us

LABARAI

Siyasar Imo: Surukin Gwamna Rochas Ya Dau Dumi

Published

on

Shugaban ma’aikata a ofishin Gwamna Rochas Okorocha, na Jihar Imo, Uche Nwosu, kasantuwarsa surukin Gwamnan Jihar ba shi zai hana shi zama Gwamnan Jihar ba.
A ranar Lahadi ne, Uche Nwosu, ya karyata zargin cewa, Gwamnan Jihar ta Imo yana mulkan Jihar ne ta hanyar sanya iyalai da danginsa a mahimman mukamai a Jihar.
Bukatar Gwamnan na tabbatar da mai auran diyar na shi a matsayin wanda yake son ya gaje shi a mulkin Jihar dai ta tsaga Jam’iyyar gida biyu, sannan kuma hakan ya jefa gaba a tsakaninsa da shugaban Jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, wanda ya ki aminta da Uche Nwosu, din shi ma. Rigimar dai ta kai ga yin zabukan fitar da gwani a Jam’iyyar gida biyu, inda kuma suka fitar da ‘yan takaran gwamna biyu.
Okorocha na cewa, “Fatan ci gaban da Jihar Imo ke da shi kadai shi ne, Uche Nwosu, ya kasance dan takara. In kuwa ba hakan ba, za a sami matsalar tattalin arziki in na sauka daga mukamin na gwamna,” in ji shi.
Bayan da aka yi ta takaddama a kan ko wane ne halastaccen dan takaran na APC a Jihar, Hukumar zabe ta lika sunan abokin hamayyar na, Uche Nwosu, watau Hope Uzodinma, a matsayin dantakaran Jam’iyyar ta APC a Jihar.
Amma daga baya sai hukumar zaben ta cire sunan na shi a jerin sunayen ‘yan takaran gwamnan da ta saki a makon da ya gabata. Kasantuwar karan da dukkanin ‘yan takaran biyu suka shigar a kotuna, inda kowannen su yake neman da a soke guda. Hukumar ta ce tana jiran umurnin kotu tukunna.
Da yake magana cikin wani shirin talabijin na Channels, a ranar Lahadi, Uche Nwosu, ya ce, baya ga shi da yake hankoron zama gwamna da kuma Rochas din mai neman zama dan majalisar dattawa, babu wani daga iyalan nasu da yake cikin majalisar gudanarwa ta Jihar.
“Batun cewa, Rochas Okorocha, yana son ya rika juya Jihar ne shi da iyalansa sam ba gaskiya ne ba.
“Ni suna na, Ugwumba Uche Nwosu. Na fito ne daga karamar hukumar Nkwerre. Rochas kuma ya fito ne daga karamar hukumar Ideato. Amma cikin ikon Allah sai na auri diyar Gwamna Okorocha. To wannan shi ne zai hana mani zama Gwamnan Jihar Imo?
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!