Connect with us

LABARAI

Abincin ‘Yan Makaranta: Hajiya Binta Abba ce Ta Karbe Mana Katin ATM -Dayyaba Ibrahim Jibiya

Published

on

Jahar Katsina na daya daga cikin jahohin da ake gudanar da wannan shiri na ba Yara ‘yan makaranta abinci, wanda yanzu haka ake ta koke akan mai baiwa gwamna shawara akan ilimi ‘ya ‘ya mata Hajiya Binta Abba dangane da abinda ya shafi biyan hakki.
Dayyaba Ibrahim na daya daga cikin wadanda aka dauka aikin yin wannan abinci a karamar hukumar Jibiya da ke jihar Katsina, sai dai ta koka game da hakkukinsu da ta ce Hajiya Binta Abba ta murkushe, amma dai ba su ya yafe ba.
Ta kuma kara da cewa lokacin da aka dauke su aiki ance su za su sayi abinci amma da aka turo masu kudade sai aka yi masu jan ido aka karbe kudadan daga hannusu, sannan kuma sai da aka sa su suka ranta kudin cefena wanda har yanzu ba a biya ba.
Dayyaba ibrahim ta ce wata rana suna jibiya sai aka kirasu sun kai su goma aka gaya masu cewa a Katsna ake nemansu da suka zo Katsina sai kawai aka wuce da su Banki suna cikin Mota aka ciye duk kudadan da aka turo masu na aikin abinci daman acewrata katin fitar da kudinsu ATM yana hannu mukaraban Hajiya Binta.
Ta cigaba da cewa bayan an fitar da kudade sai suka wuce gidan Hajiya Binta amma aka yi rashin sa’a bata nan, sai aka ce tana ofis suka je ofis din da ke tsohon gidan gwamnati sai aka baiwa kowakudin a hannunsa sai mika mata, tun daga wannan rana har yazu shiru suke ji kamar an aiki bawa garinsu.
Shin ko ya ya aka yi har katin fitar da kudadan (watau ATM) ya bar hannun masu aikin duk da cewar an gaya masu cewa kadda wanda ya sake ya bada na shi, tambayar da na yi mata ke nan sai ta kada baki ta ce?
“cewa aka yi Hajiya Binta ta ce idan ba mu bada ba, ba za a dauke mu aikin ba, shi yasa muka bada saboda muna son mu sami aikin a matsayinmu na talakawa, sannan muna ganin cewa wannan abu hakkinmu ne zamu samu ba wai kyauta bane. wannan shi ne dalili” inji ta.
Ita ma da muka tuntubi mai baiwa gwamna shawara akan ilimin ‘ya ‘ya mata Hajiya Binta Abba akan wannan zarge zarge sai ta ce yanzu haka tana Abuja wajan neman wadannan kudade da ake magana akan su. sannan ita bata da wani lamari na karbe katin fitar da kudi na masu aikin abinci.
Tuni dai yatsan zargi ke nuni da cewa Hajiya Binta na hada kai da wasu mukarabanta domin karbe katin fitar da kudi watau ATM a ya yin da wasu mata ke cewa suna ganin sakon kar ta kwana na sa masu kudi a asusun ajiyarsu na banki kafin ka kafta ido an kwashe daga wani wuri wanda haka tasa makarantun da aka ba su domin ciyarwa suke rasa abinci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!