Connect with us

LABARAI

EFCC Ta Kai Samame Gidan Dan Majalisar Tarayya A Kaduna

Published

on

Jami’an Hukumar EFCC sun kai samame a Gidan Dan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Kaduna ta Arewa, Hon. Samaila Suleiman, a Gidansa dake kawo new edtension, kusa da Rafin Guza.
Wata majiya mai tushe wacce ta bayyana a sakaya sunanta ta bayyana ma wakilnmu cewa, kai samamen bai rasa nasaba da wasikar gayyata da hukumar ta tura ma Dan Majalisar, domin yazo ya bayyana a gabanta bisa wani zargi da ake masa akan wasu tuhume tuhumr wanda ba a bayyana su ba, amma daga bisani Dan Majalisar yai kunnen Uwar Shegu da wasikar.
Jami’an Hukumar EFCC sun kai samamen Gidan Samaila Sulaiman ne da misalin karfe 10 na safe, a inda suka yi awon gaba da wasu masu aikinsa har su uku, wanda daga bisani bayan dogon rubuce rubuce, aka sako su.
Sai dai duk kokarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin Hon. Samaila Sulaiman, abin yaci tura, domin ya kira shi a waya, bai same shi ba, kuma ya tura masa sakon test, amma babu amsa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!