Connect with us

TARIHI

Mafarin Wa’azin Maitatsine Da Almajiransa

Published

on

Mun samu tangarda a makon da ya gabata wurin wallafa shafin nan saboda ajizanci na Dan Adam, muna fata ku gafarce mu. A halin yanzu mun gyara kuma ga maimaitawar shafin kafin mu cigaba a mako mai zuwa.
Masu karatu assalamu alaikum. A wannan makon za mu kawo muku bayanan daya daga cikin mutanen da suka san Maitatsine saboda makotakar da suka yi da shi inda a ciki za ku ji yadda Maitatsinen ya fara fita wa’azi har kuma daga bisani ya fara tura almajiransa bayan ya hamshaka. Za ku ji sunan wanda ya yi jawabin daga bakinsa, da yake an ce ‘waka a bakin mai ita ta fi dadin ji’.
“Assalamu Alaikum warahmatullahi Ta’ala wabarkatuh. Sunana Abdullahi Ja’afar wanda aka fi sani da Abdullahi Dan Fagge.
“To Maitatsine dai bani da wata Alaka da shi sai dai soyayya ta irin da a yanda almajiri yake idan ya ga malami da yake tara almajire ake karatu. To idan ya ganni yake sha’awa shima sai ya dunga ina ma yana da irin wannan karatun shi ma ya zama cewa yana da Alkur’ani domin makaranta ce da za ka ga yara kananu kamar ‘yan shekara takwas, Tara goma zuwa shabiyar ka ji suna karatun Alkur’ani sai ka ji wannan abu yana burgeka. Saboda ita makarantar Maitatsine akan hanya take, idan ka tawo daga unguwar Fagge, ‘yan’awaki, koki duk za ka sameta akan hanya duk wanda zai wuce ta kofar makarantar zai shige, wannan yasa shi Malam Maitatsine akwai wata mace da ake kira mama maiganye take saida tuwo a lokacin.
“To saboda haka ya Auri wata yarinya a gidan kullum zai zo ya wuce ta bakin makarantar mu, muna zaune a cikin gidan Alhaji Nasiru Ahali. A nan muke shinfida muna kallon yamma, akwai wani mutun da ake ina jinsa a radiyo ana kiransa da suna Alhaji Nasiru Ibrahim Shehi Zamani, Jagoran Falasdinawa to idan yamma ta zo kofar gidan mahaifinsa muke zuwa muyi shinfida mu zauna mu yi karatu wanda ake kira Alhaji Ibrahim ‘ci ka koshi nufin Allah ne’ ko a ce Alhaji Ibrahim koki kusan dai wannan bawan Allah ya rasu, amma akwai ‘ya’yansa irin su shi Shehi Zamani Jagoran Falatsinawa irin su Auwalu tariya da dai sauransu ya’yansa suna nan Allah ya yi musu albarka Allah ya tsare masa su.
“To idan Maitatsine ya zo zaizo gurin Malam Sale sai su zo su gaisa malami da malami Alaramma da Alaramma, kullum kuma yana tare da kamar a ce magoya bayan sa mutun biyu suna take masa baya sai shi Malam Audi ya taso su gaisa, sannan sai ya wuce gidan wannan surukar tashi su gaisa idan ya dawo sai ya kuma zuwa a yi masabiha da hannu, sannan ya koma gidansa, wannan ya sa kullum haka ake yi, saboda haka ya sa nasan Maitatsine ciki da bai gabada baya.
“Sannan Maitatsine suna da alaka ta cewa babban malami da babban malami saboda ita Ariyar nan ta Koki da Yan’awaki akwai wasu manya manyan makarantu a yanki, kamar irin makarantar shi Malam Sale malamin mu kenan , sannan akwai Malam Ibrahim, akwai su Malam Audu, akwai irinsu Malam Musa , akwai kuma wani babban malami a unguwar wanda ake kira Malam Gwani Dan Zarga. To sannan dai makarantu manya manya wanda ko wanne irin wannan Alaka almajiri ya san wadannan manyan malamai ne, amma in ban da wannan babu wata alaka ta fahimtar juna. Kowanne Almajiri a makarantarsu daban Al’adun su daban al’amuransu daban yanzu kamar akwai wata makaranta da ake ce mata makarantar sokotawa wadannan dama a lokacin al’adunsu kusan ya sha bamban da kowani Almajiri da yake wannan Ariyar. Amma in ba haka ba babu wata Alaka da take ta wani abu daban.
Shi Maitatsine mutunne wanda yake da yana tafiya yawo wa’azi. An san shi in ya fadi kalma sai ya ce “Allah ta tsine su masu jin radiyo a gida ko Talabijin, Allah ta tsine su”, da dai duk wanda ya ajiye kayan da bature ya kera, duka ‘Allah ta tsine su’. Wani lokacin kuma yana zuwa bakin kwangiri inda yanzu ake kira IBB way, a nan yake wa’azi kullum za ka gan shi da doguwar Riga kuma mutum ne baki dan Siriri, amma ba siriri can ba, nan yake zuwa. Saboda haka duk wadansu manyan malamai yana da wata ma’amala da su mai kyau, amma daga baya sai ya samu wani al’amari ya shigo masa daban. Yana da makotaka da Alhaji Danlami Alhassan, gidansu Katanga daya, yana da makotaka da Alhaji Yawale gidansa da yake ‘Yan’awaki , yana da makotaka da gidan Yarabawa, yana da makotaka da wani Alhaji Danjummai. Wannan ya sa ana ma’amala mai kyau a lokacin amma shi lokacin Maitatsine sallah ma ba ta dame shi ba, dan akwai wani masallaci wanda Alhaji Yawale ya gina wanda shi babban su Auwalu da Sani yake limanci.
“A wannan gurin Maitatsine ba ya zuwa ya yi sallah kuma a gidan nasa ma shi ba za ka ga yana sallah ba ba ta dame shi ba. To yau da gobe yana zuwa wannan wa’azi, da ya hamshaka ya zama babban mutun ya bunkasa sai kuma ya koma tura Almajiran sa su je su yo wa’azi su dawo, irin abin da ake bayarwa na sadaka su suke kawowa da ‘yan sauran Almajiran sa masu yankan farce irin su suke kawo wa masu washin wuka da sauran duk wasu abubuwa da in sun samo suke kaiwa. Ya ta’allaka da su ne yake samun kudin shiga. To wannan abubuwan ya sa Maitatsine ya hamshaka kuma da yake a lokacin masu kudi sukan bashi kudi a yi masu Addu’a.”
To Jama’a a nan za mu dakata sai sati mai zuwa za mu ci gaba Insha.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!