Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Muna Yi Wa Matan Da Basu Da Kudi Fyade –Dan Fashi

Published

on

An samu nasarar cafke mutum biyu bisa zargin su laifin fashi da makami tare da yi wa wata mata mai shekaru 34 fyade a sassanin Fulani na Gadan Eregi a kan titin Bida cikin jihar Neja. Majiyarmu ta labarta mana cewa, wadanda ake zargi su ne Umar Audu dan shekara 50 da kuma Umar Mohammed mai shekaru 40, dukkan su daga sassanin Fulani na Gadan Eregi, rundunar ‘yan sanda reshan Kataeregi cikin karamar hukumar Katcha su ne suka samu nasarar cafke wadanda ake zargin. Majiyar tamu ta bayyana mana cewa, wadanda ake zargin sun farmaki wannan mata ne da adda da kuma gura, inda suka nemi ta basu naira 400,000. Lokacin da ta ki basu, sai suka ja ta daji suka yi amfani da ita da karfi.

Daya daga cikin wanda ake zargi mai suna Audu ya bayyana wa manema labarai cewa, muna yi wa matan da basu bamu kudi ba fyade. Ya kara da cewa, “Idan muka shiga gida, sannan masu gidan suka ki bamu kudin da muke bukata to sai mu yi wa duk wata mata da muka samu a cikin gidan fyade a matsayin abun fansa. Ba ruwan mu da cewa karace ko kuma tsohowace, indai ba a bamu kudi ba to sai mun yi amfani da wata mata a cikin wannan gida. “Indai mai gida ya yi mana taurin kai to sai mun yi amfani da matarsa ko kuma diyarsa.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja Muhammad Abubakar ya bayyana cewa, wadanda ake zargi sun amsa laifin su, ya kara da cewa, za a mika wadanda da ake zargi zuwa kotu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!