Connect with us

HANGEN NESA

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga ’Yan Boko Haram

Published

on

Na rubuto muku wannan wasika ne saboda nasan zata isa inda ku ke, kuma sakona inada tabbacin zai yi tasiri matuka a gurinu. Ya ku ‘yan barandan kungiyar fafutukar kafa gwamnatin Musulunci wannan fili mai taken HANGEN NESA yana tattaunawa ne akan matsalolin da suka addabi wannan kasar, musamman bangaren siyasa, kasuwanci da kuma tsaro. Matsayina na marubucin shafin Mailafiya, na ga ya dace in rubuto muku wannan budaddiyar wasika, domin in kara tunasar daku halin da hare-haren ku yake jefa al’ummar kasar nan, da kuma yadda kuka sanya musulmai cikin zulumi da kuma yadda ake daukansu matsayin ‘yan ta’adda.

Ya ku ‘yan Boko Haram (kamar yadda akafi gaya muku) kusani duk wani bincike da ilimi na Musulunci babu inda ya ce ayi jihadi ta hanyar kashe wadanda suka karbi addinin Allah, suna sallah, suna azumi, suna kuma duk wata ibadar da addini ya halasta, babu inda Allah yayi umarni da ayi yankan rago ko kisa ga abokan zama wadanda basu karbi sakon ba, saboda haka ne ma ya aiko Annabawa, ya kuma sanya musu hikima ta zance da basu littafi amatsayin wanda zai nuna aikin da suka zo yi ban kasa, da ana kashe al’umma hakanan, da an aiko malaku tunda wuri sun karkashe mutanen Annabi Nuhu (A. S) amma saboda shi Addinin Allah yana son zaman lafiya da kwanciyar hankali, sai ya ce ayi kira zuwa addinin gaskiya, wannan shi ne babban jihadin da Addinin Allah ya amince, duk da ni dalibin ilimi ne, amma kai tsaye zan iya cewa abinda ku ke ba shi ne ainihin jihadi da Addinin Musulunci ya yi koyi ba. Wannan kenan.

Ya ku wadannan mutane, kun yi amfani da sunan Musulunci, kun kashe rayukan da ba za su kirgu ba, kun kashe mutane suna Sallah, kun kashe mutane suna tafiya zuwa guraren sana’ar su ko makaranta, na dauka idan Addinin Allah ku ke karewa, bazaku kashe ‘yan uwanku ahalin bautar Allah ba, kuma Ubangijin da kuma kuka yadda dashi, kuma ku ke da’awar yin jihadi don daukaka Addinininsa. Shin kunada masaniyar cewar kun maida mataye zawarawa, kun maida yara marayu, kun maida gidaje kufe, kun sanya hawayen mu yafara kafewa saboda yawan zubewa da yake, kun kashe dakarun kasa dake kare al’ummar kasa ? Don Allah wannan wace iriyar jihadi ce ku ke yi, wace iriyar littafin Addini ku ke karantawa wanda yake umartar ku dakuyi wannan aikin ?

Amatsayina da dan kasa, mai kishinta da kuma kokarin komai ya tafi daidai, ina amfani da wannan damar da nike da ita ta isar da sako. Ina kiranku da ku ji tsoron Allan daya halicceku, ku ji tsoron haduwa da Ubangijin daya halicceku, wanda zai yi hisabi akan duk ran da kuka kashe, ku ji tausayin al’ummar da ku ke kassarawa, ku ji tausayin musulmai da ake hantarar su saboda ku, ana cewa su ‘yan ta’adda ne, ku yadda ayi maslaha tare da ajje makaman ku tun kafin a karar daku, sojojin mu masu tarin yawa da kuka kashe, mutanen da ku ka kama ku ke azabtarwa, ‘yar uwarmu da ku ka kashe (Hauwa Liman) kwanakin nan za su sanya gwamnati takara daukan wasu matakan gaggawa akanku, ku ji tsoron Allah ku fadi wadanda ke daukar nauyinku, ku ji tsoron Allah ku tsayar da ayyukan kashe al’umar da ba su ji ba, kuma basu ganiba, amma kun kashe ahalinsu, danginsu kuma kun rabasu da gidajen su da garuruwan su.

Ya ku ‘yan boko haram, mun sani cewar akwai wasu makiyan kasa da suke amfani daku, kuma suna daukar nauyin ku, munsan cewa kayan da ku ke aiki dasu kuna daukan rayukan al’umma, lalle akwai wasu ‘yan siyasa, turawa da masu kudi da suka san wannan ta’asar da ku ke, kuma suke temaka muku, saboda basusan kasancewar NIJERIYA dunkulalliyar kasa, tashin hankali da rashin zaman lafiya sune ababen sonsu, ku ji tsoron Allah ku fallasa su. Ina kira agareku da kuka kara karanta zancen ubangiji (Alkur’ani mai girma ) na tabbata zaku gane cewar abinda ku ke aikatawa yayi hannun riga da sakon Ubangiji, na tabbata za ku yi dana sani da zubar da hawaye bisa wannan ta’asar da kuka aikata, kuma ku ke kan aikatawa.

Ina kara kiranku da cewar ku ajje makaman ku, kubar wannan bakar sana’ar ta daukan rayukan al’umma. Saboda biyayya da kauna da Addinina ya sanya dole in gayawa duniya cewar abinda ku ke baya daga cikin sakon Ubangiji ga mabiya addininin sa, sannan kishin kasa ta, da kuma kaunar zaman lafiya da kullum muke wa’azin sa, ya sanya ni rubuto muku wannan budaddiyar wasika, don nasan babu abinda zai hanata isa inda ku ke, kuma na tabbata Allah ya hore muku ikon fahintar yaren hausa da zaku fahinci duk wani sako da yake ciki daki-daki.

Allah Ubangiji ya sanya wannan wasika tayi tasiri gareku. Allah ya sanya ta zama silar shiryuwar ku ko kuma wasu daga cikinku. Allah ya sanya wannan wasika ta zama silar dawowar zaman lafiya a kasata tare da kawar da ayyukan ‘yan Boko Haram, Ameen.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!