Connect with us

MANYAN LABARAI

Yan Majalisar Wakilai 3 Sun Fice Daga Jam’iyyar APC  

Published

on

A yau Alhamis ‘yan majalisar wakilai hudu suka ayyana ficewar su daga jam’iyyar APC mai mulki, a yayin da dan majalisar jami’iyyar PDP daya ya fice daga jam’iyyar, ‘yan majalisar sun ayyana ficewarsu daga jam’iyyun ne a wasiku daban-daban da suka mika wa shugaban majalisar da safiyar yau Alhamis, inda shugaban majalisar, Yakubu Dogara ya karantawa zauren majalisar wasikun ‘yan majalisar.

Mutum ukun da suka fice daga APC mai mulki sune, Adekunle Akinlade, mai wakiltar Egbado ta kudu a mazabar tarayya a jihar Ogun, wanda ya koma jam’iyyar APM, sai Muhammad Ajanah mai wakiltar mazabar tarayya ta Adavi dake jihar Kogi, wanda ya koma jam’iyyar PDP, Mista Salis Koko mai wakiltar mazabar tarayya ta Koko dake jihar Kebbi kuma ya koma jam’iyyar SDP daga APC.

Shi kuma Rabiu Kaugama ya fice ne daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar SDP, Kaugama shi ne yake wakiltar mazabar tarayya ta Malam Madori da Kaugama da ke jihar Jigawa, dukkan ‘yan majalisun hudu suna korafi ne akan yadda jam’iyyun nasu suka gudanar da zabukkan fidda gwani a kwanakin baya.

Ana yawan samun canja sheka daga jam’iyyu musamman a tsakanin ‘yan majalisar wakilai, mafi yawan ‘yan sitasar da suke canja shekar wadanda basu samun tikitin tsayawa takara bane a jam’iyyun da suke, don haka suke canja sheka zuwa wasu jam’iyyu don tsayawa takarar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!