Connect with us

BIDIYO

Wasu Muhimman Abubuwan Da Ba Ku Sani Ba Kan Mawaki Sunusi Musa

Published

on

A yinkurin mu na cigaba da kawo muku abubuwan dasu ka shafi rayuwar mawakan mu na Hausa Hip Hop dake wakiltar kasar mu, al’adun mu, da harshen mu a idon duniya ta hanyan wakokin su masu nishadantarwa, fadakarwa dakuma ilmantarwa ne yasa muka ga dacewar binciko muku wasu abubuwa masu mahimmanci akan rayuwar wadannan mawakan domin mu da ku masoyansu mukara sanin su tare da goya musu baya a harkonkin su na Hausa Hip Hop. Dan haka muka yi bincike akan daya daga cikin manyan mawakan Hausa Hip Hop dake jahar Kaduna kuma wanda tauraransa ke cigaba da haskawa a wannan masana’antar ta Hausa Hip Hop. “S>BOI NE”  babu shakka dayane daga mawakan da suka shahara a Arewacin kasan nan musanman a harkar wakoki da kuma Rawa.

A ranar 1 ga October na shekarar 2018 ne ya saki sabuwar wakarsa kuma ta biyar a wannan shekarar ta 2018 mai suna “Yar Kaduna” bayan kammala makaranta da ya yi a cikin shekarar nan.

Mun binciko muku abubuwa guda goma daga cikin abubuwan da baku sani ba akan mawakin kuma sune kaman haka:

1- Bahago ne S.boi, da hannun hagu yake rubutu, da kuma kafar hagu yake kwallon kafa musanman abaya chan lokacin da mawakin yake buga gaba a makarantar primary da secondary din daya gama, inda ake kiran sa da suna “C.Boi Ne” kafin daga bisani ya koma “S.boi Ne” bayan ya fara waka.

2- dika primary school din da S.boi yayi da secondary school din da mawakin yayi a Unguwa Rigasa na Kaduna suke. Wato Island International School inda anan ne ya sami sunan sa na “C.boi Ne” da kuma G.S.S Rigasa inda yayi Secondary School dinsa. Duk a ungwar Rigasa dake a karamar hukumar Fagge dake nan jahar Kano inda kuma a wannan ungwar ta sabon gari aka haifi Dabo Daprof a Danbata way dake kusa da gidan kallo na Eldarado dake sabon gari.

3- Ba bahaushe bane, duk da shahara da Dabo Daprof yayi a masu waka da harshen Hausa musanman na Hausa Hip Hop anan arewacin Nigeria, da yawa daka cikin mutane basu san cewa S.boi ba Bahaushe bane ba. Yaren sa na asali shine “SHUWA ARAB” daga jahar Maiduguri dake Nigeria amma a jahar Kaduna aka haifi mawakin, a Kaduna ya girma kuma har yansu a Kaduna yake zaune. Kuma yana waka da yare akalla guda shida wanda duk a Kaduna ya koye su.

4- S.boi yana da Inkiyoyi da yawa, sunan mawakin na haihuwa shine SUNUSI MUSA IDRIS amma Inkiyoyin sa sunfi 50 kuma sanannu daga ciki sun kai 10, ga wasu daga ciki:

S.Boi Ne

Swags Man

NRML Lebel

Gangariya

Shuwa Boi.

SMBSKid

Ko Ba Kowa Akwai Allah

Dan Arewa

Da dai sauransu.

5- Shine mawakin Hausa Hip Hop na farko daya fito a finafinan turanci guda biyu na Kannywood industry kuma irinsu na farko a tarihin masana’antar.

6- S.boi yafi son Facebook chat akan sauran social networks shiyasa yafi dadewa akan Facebook chat fiye da sauran chats.

7- Shine daya daga cikin mawaka hudu a tarihin Hausa Hip Hop da suka yi zangazanga lumana a kafafan sadarwa na zamani akan naimawa mawakan Hip Hop na jahar Kaduna inchin saka wakokin su da gidajan radion Karama fm da Wazobia fm basayi. Kuma bayan zangazangan yasamu goyan bayan masoyan Hausa Hip Hop, gidajan radion biyu sun kirkirri sabin programs dasuka fara saka wakokin mawakan Hausa Hip Hop din.

8- Wakar sa ta farko a duniya itace “Baby Girl” kuma yanzu haka ta pata a wayoyin mutane, domin babu mai wakar yanzu. Kuma mawakin yana bakincikin rasa wannan wakar.

9- Shine mawaki na farko a tarihin mawakan Hausa Hip Hop na Kaduna daya fara rubuta littafi mai suna “In Da Rai” kuma Littafi na farko da aka rubuta ta da kafiya tundaga farko har zuwa karshe.

10- Wakokin S.boi da yayi shi kadai guda uku ne kawai izuwa yanzu, su ne Gida Arewa da Shake Ur Body da ’Yar Kaduna.

11- S.Boi mutum ne mai son zaman lafiya da zama cikin abokai koda yaushe, kuma shi injiniya ne na Motocin zamani.

12- Ya kware sosai a rawa, a rawa kadai ya samu kyaututtuka na lambar yabo guda uku.

13- bai yi aure ba amma yana da budurwan da ya tsayar zai aura.

14- babban abokinsa da suke tare da shi kusan kullim sunansa Aminu amma an fi saninsa da Fc Santos.

Amma adadin wakokin da mawakin yake aciki bazasu lissafu ba.

Wadannan sune kadan daga abubuwan ban mamaki da sha’awa akan rayuwar mawakin Hausa Hip Hop wato S.Boi Swagzman. Fatan kun karo, kun ilmantu kuma kun nishadantu da wadannan abubuwa guda goma da muka binciko muku akan mawakin.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: