Connect with us

RAHOTANNI

Kungiyar CLO Ta Karrama Gwamna Ganduje A Matsayin Gwamna Abin Koyi

Published

on

Ya yinda jama’a ke ta kara nuna farin ciki da yadda ake ta baiwa Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje lambobin yabo daga sassa daban daban na kungiyoyin ci gaban al’umma, a wannan karon ma Gwamnan ya kara yin hafzi da wata gagarumar lambar yabon.

Wata gawurtacciyar kungiyar kare hakkin dan adama ta Cibil Liberties Organisation wadda aikinta shi ne tabbatar da gaskiya da daidaito ta karrama Gwamnan da wannan babbar lambar yabo kan kasancewar gwamna abin koyi ta fuskar yiwa al’umma hidima, musamman saboda kokarin da yake wajen ci gaban harkokin ilimi, Lafiya, samar da kayan more rayuwa, bangaren inganta harkokin shari’a, zaman lafiya da tsaro a Jihar Kano.

Da yake jawabi a lokacin taron da aka gudanar a Otal din Cubana dake Abuja, shugaban Kungiyar ,Igho Akeregha ccewa ya yi wannan shi ne tarihi tun kafuwar wannan kungiya a shekara ta 1987 wadda Jihar Kano ta tabbatar, bayan shekaru 19 da demkaradiyyar Najeriya ta kasance batare da yankewa ba, muka ga da cewar aunawa tare da yabawa wadanda suka bada gagarumar gudunmawwa ga ci gaban al’ummarsu.

Ya ce a shekaru biyu da suka gabata Gwamna Ganduje ya samu nasarar  gudanar da cikakken jagoranci ta hanyar samar da tallafin inganta rayuwar Matasa da kuma farfado da harkokin tattalin arzikin Jihar Kano.

Ya ce Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje shi ne Gwamna na farko wanda wannan kungiyar ta baiwa lambar yabo, saboda haka  muke fatan zai ci gaba  isar romon demokaradiyya  ga al’ummar Jihar Kano.

Da ya ke karbar lambar yabon Mataimakin Gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna wanda shine ya wakilci Gwamna Ganduje, cewa ya yi muna matukar farin cikin karbar wannan gagarumar lambar yabo daga wannan shararriyar kungiya ta CLO.

Ya ce na tsaya anan cikin karsashi domin karbar wannan babbar lambar yabo daga wannan kungiya wadda ta shahara waje tsage gaskiya  da kuma tsayawa haikan wajen yakar zalunci

Hakazalika Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya jaddada farin cikinsa ga kungiyar CLO bisa samar  da wannan kyakkyawan tsari da zai taimakawa shugabannin wajen yin aiki tukuru domin daukaka darajar jama’ar su. Don haka sai ya tabbatarwa da Jama’a aniyar Gwamnatin Kano na hada karfi da kungiyar ta CLO don ciyar da Jihar Kano gaba, musamman yakin da take na kawar da matsalar shaye shayen miyagun kwayoyi  domin samar da nagartattun matasa a nan gaba. Kamar yadda mai Magana da yawun Mataimakin Gwamnan Kano Malam Hassan Musa Fagge ya shaidawa Jaridar LEADERSHIP A Yau.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: