Connect with us

SIYASA

Siyasar Zamfara: Yadda Sanata Marafa Ya Yi Wa Gwamna Yari Ritayar Dole

Published

on

Wani ya taba tambaya ta, wai mene ne silar sabanin da ya afku tsakanin Gwamna Yari da Sanata Marafa? Amsar da na ba shi ita ce, sabanin ya samo asali ne daga yunkurin bambancewa tsakanin karya da gaskiya. Sabani ne da tun asalinsa a bayyane yake ga kowa, tamkar yadda hasken rana yake bullowa duhu ya gushe.

Wannan rashin jituwa ya faro ne yayin da wani mutum, wanda shi ne shugaban tsaro na jiha, kuma lamba dayan Jihar Zamfara ya wawitar da kujerarsa, ba wai don bai san hanyar da zai bi ya rike ta ba, a’a, sai dai don zuciyarsa ta cika da son rai.

Sai ya kasance wannan shugaban tsaro na jihar ba shi da aiki sai yawo, kai kace wanda ya ci kafar Kare. Kullum yana jibge a Abuja, kamar wani Minista ko ma’aikacin tarayya mai zaman ofishin Abuja. A wata ingantacciyar ruwayar ma an ce, ya kan yi wata guda cur bai leka jihar da yake shugabanta ba. Sannan kuma akwai tabbacin cewa, bai taba yin kwanaki na mako guda cur a cikin Jihar Zamfara ba.

Wannan sakaci da rashin sanin inda kai ke ciwo ne ya sa ‘yan bindiga suka mayar da Jihar Zamfara tamkar wata tashar barna da kasuwar baje kolin rashin mutunci, rashin imani da keta haddi.

Lokacin da asharararru suka fahimci cewa, Jihar a sake take kamar ba gwamnati, sai suka bude shafin kisa, garkuwa, satar mutane, da fashi da makami. Dama tun kafin su fara ta’asar tasu, sai ma’aikatan jiha su kwashe watanni ba tare da sun ji labarin albashi ba.

Sai da ta kai an shiga wani yanayi na la haula a Jihar Zamfara. Mafita kawai al’umma k enema. Har ma ta kai ba wai kawai mafitar ba, wanda zai yi magana al’umma ke muradi. A irin wannan yanayi ne, Sanata Kabir Marafa, sanata Mai Wakiltar Zamfara  ta tsakiya ya mike tsaye, ya fara kalubalantar irin rikon sakainar kashin da gwamna Yari ke yi wa Jiharsu ta zamfara.

Duk da yake akwai ‘yah majalisa dattawa uku ne a fadin Jihar Zamfara; Dan majalisar dattawa mai wakiltar Zamfara ta Yamma; Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Zamfara ta Arewa, da kuma kujerar Marafa wacce yake wakiltar Zamfara ta Tsakiya.

Duk wadannan ‘yan majalisa da na lissafo babu wanda ya taba cewa uffan dangane da irin rikon ko-in-kula da gwamna Yari yak e yi wa Jihar Zamfara. Saboda suna kiyaye shiga takun saka da gwamna, ko kuma saboda wani dalilin nasu na kashin kansu.

Shi kuwa Sanata Kabir Garba Marafa, a haka ya jajirce, babu wani abu da ya iya tsorata shi balle ya rufe baki, ko ya kawar da kai ga irin halin kuncin da al’ummar Zamfara ke ciki.

Ya mike a majalisa ya bayyanawa duniya irin halin da jihar ke ciki, da kuma irin cin kashin da ‘yan bindiga ke yi wa al’umma. Wanda a lokaci guda kuma Gwamnan Jihar babu ruwanshi, bai ma nuna halin damuwa ballantana nadama.

Wannan magana ce babban zunubin da Sanata Marafa ya aikatawa gwamnatin Abdul’aziz Yari da mukarrabanta. Su a warin mutanen gwamnatin Yari, me zai sa Sanata Marafa ya furta irin wadannan kalamai a gaban majalisa. Wai, inji su, magana ce ta cikin gida.

Kun ji fa! Ana batun kisan mutane, amma susuna batun wai maganar cikin gida ce da bai kamata a fitar da ita ba.

Yayin da suka tsananta gaba da kiyayya ga Sanata Marafa, shi kuma a gefe guda yana ci gaba da wayar da kawunan jama’a dangane da irin abubuwan da ke faruwa a Jihar Zamfara. Irin rashin da’a da rashin mutunta rayukan dan adam da gwamnati ke yi. Wannan ne babban dalilin da ya sa sanata Marafa ya sha alwashin ko ta wane hali sai ya yi wa Gwamna Abdul’aziz Yari da duk wani mai irin ra’ayinsa ritaya daga siyasar Jihar Zamfara.

Da farko sun dauki wannan kuduri na Sanata Marafa da wasa, har ma suna yi mishi izgilin wai ya haukace. Amma da tafiya ta yi tafiya, sai suka fara Ankara cewa wannan maganar da Marafa yake yi fay a dauke ta da gaske.

Sun yi ta bin hanyoyin da za su fusata shi ya fice daga jam’iyyar APC, amma da yake ya fi su wayo a siyasa, ya kuma fi su sanin dabarunta. Har akwai wani abu da ya taba faruwa ma. Lokacin da aka yi babban taron jam’iyyar na kasa a watannin baya, sai gwamnatin Jihar Zamfara ta shirya tuggun inda aka hana duk wasu magoya bayan Sanata Marafa shiga filin taron na ‘Eagle Skuare’.

Kafin nan ma akwai wani abin da ya faru. Lokacin da ake zaben shugabannin jam’iyyar APC na jihohi, kananan hukumomi da gundumomi ma sai da gwamna Yari ya yi iya kokarinsa wurin kakaba shugabannin da yake ganin za su biya mishi bukatunsa idan lokacin zabe ya zo. A sannan ma sai da Sanata Marafa ya yi fito na fito da wannan rashin gaskiya, inda shi ma ya gudanar da zabensa daban.

Da aka zo gab da zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, wanda daga nan za a fid da ‘yan takara. Sai Yari ya dage a kan sai dai a yi amfani da tsarin zaben wakilan jam’iyya ‘Indirect Primaries’, shi kuwa Sanata Marafa ya ce, atafau sai dai fa a yi amfani da tsarin ‘yar tinke ‘Direct Primaries’.

Wannan ne mafarin turmuza hanshin gwamna Yari da mukarrabansa da kasa. Inda Sanata Marafa ya nuna musu cewa shi halastacce ne, kuma mai magana da cikawa. Karshe sai ga Uwar jam’iyyar APC ta fidda sanarwar cewa zaben wasu jihohi ciki har da Zamfara za a yi ne amfani da tsarin ‘yar tinke (kato bayan kato).

Tun daga wannan lamarin Gwamna Yari ya fara shiga taitayinsa, ya kuma sha jinin jikinsa kan cewa batun yi musu ritaya daga siyasa fa ya fara tabbata.

Yanzu haka murna al’ummar Jihar Zamfara suke yi, ganin cewa Gwamna Yari da mukarrabansa sun fara numfashin karshe a tarihin siyasar Jihar Zamfara. Gwanin talakawa, kuma gwanin al’ummar Jihar Zamfara, Sanata Kabir Garba Marafa ya cimma nasara a wannan yaki da munanan manufofin gwamnatin jiha. Duk inda ka bi a fadin jihar zancen kenan, an yi wa Yari ritayar dole a siyasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: