Connect with us

SHARHI

Alhaji Dahiru Mangal: Halin Mutum Jarinsa

Published

on

A ranar Asabar daya ga watan Nuwamba na wannan shekara ta 2018 jami’ar Al-Hikmah da ke birnin Ilori ta yi bukin yaye dalibanta da suka safke karatu tare da karrama wasu mihimman YanNijariya da digirin girmamawa wadanda suka bayarda gudunmuwa iri daban daban wajen ciyar da wannan kasa a gaba.

Daga cikin  mihimman mutanen da aka karrama akwai shahararren Dan kasuwar nan kuma mai taimakon al’umma da ke a garin Katsina watau Alhaji Dahiru Bara’u Mangal.

Mangal kamar yadda aka fi kiranshi,  ya kasance daya daga cikin mashahuran yankasuwa masu arziki da suka dade suna jan zarensu a harkokin kasuwanci da siyasa ba a Arewa ba kawai a dukkan fadin Nijariya da jamhuriyyar Nijar.

Mangal ya kasance Dankasuwar da sunanshi yayi fice a ciki da wajen jihar Katsina har da kasashe makwabta irinsu Jamhuriyyar Nijar , Benin , Mali , Togo da Burkina Faso, sakamakon alheri , kyauta, hakuri da taimakon jama’a.

Ta fuskar taimako, Alhaji Dahiru Mangal ya shahara wajen taimakon jama’a da taimakon addini duk da cewar baya son ana bayyanawa. Haka nan ta fuskar kyata ma ya tserewa duk wani attajiri da aka ta6a yi a jihar Katsina. Batun mutanen da ya biyawa kudin kujerar Makkah da Umrah kuwa Allah kawai yasan iyakarsu domin sun wuce lissafin mutum.

Ta fuskar hakuri kuma , komi kiyayyar mutum da Alhaji Dahiru Mangal tilas ya yaba ma shi , domin har yau har gobe babu baya da abokin fada ko wanda suke shari’a akan yana bin shi bashi. An shedi cewar Mangal yakan rama alheri akan sherri da ake yi ma shi. Sannan ya kan yafe bashi ga wadanda Allah bai horewa abin biya ba.

In ban da  gwamnati babu wani mahaluki a duk  fadin jihar Katsina da ya kai Mangal samarwa al’umma hanyar cin abinci ta hanyar kamfanonin da ya mallaka. Wadannan kamfanoni sun hada da kamfanin sufurin jiragen sama na Mad Air , wanda a yanzu babu kamarshi a fadin kasar nan da Kamfanin gine gine na AFDIN da  kamfanin sufuri da kamfanin hadahadar Man Fetur na Masanawa da sauran su. Haka nan kuma Alhaji Dahiru Mangal ya mallaki manyan Filazoji a manyan biranen kasar nan irinshi Abuja , Kano , Kaduna, Katsina da sauransu wadanda mutane da yawa ke neman abinci a cikinsu.

Tun bayan komawa ga mulkin Damakuradiyya a shekarar 2019 , Alhaji Dahiru Mangal ya shiga tsundum cikin harkokin siyasa. An kuma ci gaba da damawa da shi a siyasar jihar Katsina da siyasar tarayyar Nijariya tun daga wancan lokacin har zuwa yau.

Ya kasance amini kuma abokin tafiyar tsohon gwamna kuma tsohon shugaban kasa watau marigayi Alhaji Umaru Musa Yar’adua. Siyasar Alhaji Dahiru Mangal ta kara karfi a shekarar 2003 a lokacin da shugaban kasa na yanzu ya kawo guguwar canji a karon farko a karkashin tsohuwar jam’iyyar ANPP. Z

Wannan guguwar ta yiwa jam’iyya mai mulki a jihar Katsina watau PDP 6arna a za6en 2003, inda ta amshe kujerun Sanata guda biyu da kujerun majalisar tarayya dana majalisar jiha masu yawa.

Mutane sunyi ammanar cewa da za6en gwamna aka fara gudanawa kafin za6en majalisar tarayya to da Marigayi Umaru Musa Yar’adua bai kai labari ba. Ganin yadda jam’iyyar adawa ta ANPP a wancan lokacin ta yiwa jam’iyyar PDP mai mulki wakaci-ka-tashi a za6en majalisar tarayya da aka fara gudanarwa.

Babu shakka Alhaji Dahiru Mangal ya taka mihimiyyar rawa wajen murkushe duk wata barazana da marigayi Alhaji Umaru Musa Yar’adua ya fuskunta a yunkurinshi na komawa kujerarshi a karo na biyu. Wannan dalili yasa likkafar Mangal tayi gaba inda ya zarce duk wani tsohon Dansiyasa a fadin jihar ta Katsina.

Sakamakon haka ne , marigayi Alhaji Umaru Musa Yar’adua ya baiwa Alhaji Dahiru Mangal mukamin GOC watau ( General Officer Commanding ) na siyasar jihar Katsina baki dayanta.

A shekarar 2007 ma , bayan da aka tsayarda marigayi Alhaji Umaru Musa Yar’adua takarar shugaban kasa likkafar siyasar Alhaji Dahiru Mangal tayi ta kara yin gaba ta kai kololuwa inda ta kai a matakin tarayya. Duk inda marigayi Alhaji Umaru Musa Yar’adua yasa kafa wajen yakin neman za6e na shugaban kasa da shi aka je har Allah ya ba da nasara.

Bayan rasuwar Alhaji Umaru Musa Yar’adua, mutane da yawa sunyi tsammani cewar siyasar Alhaji Dahiru Mangal ta zo karshe , amma  ba haka yake ba. Domin ya cigaba da yin tasiri a siyasar jihar Katsina da siyasar tarayyar Nijariya.

Kazalika bayan tasowar guguwar canji karo na biyu a shekarar 2015 , mutane sun yi tsammani karshen siyasar Alhaji Dahiru Mangal ya zo. Amma da ya ke an ce, ‘Zakaran da Allah ya nufa da cara , ko ana Mazuru ana Shaho sai ya yi’. Sai ga shi kuwa Alhaji Dahiru Mangal bai yi kasa a gwiwa ba wajen yadda da kaddarar Allah ba, inda ya bi guguwar canji  aka canza tare da shi.

A dalilin haka sai siyasar Alhaji Dahiru Mangal ta kara karfi fiye da lokacin baya. Masu tunanin cewa zaren Mangal zaya tsinke , sai suka ga ya koma rodi. Domin Mangal ya kasance na hannun daman gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari tare da shugaban kasa Muhammad Buhari.

A wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da aka gudanar kwanakin baya a gidan gwamnatin jihar Katsina , gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bugi zuciyar wadanda Mangal ya tsonewa ido. Inda ya bayyana gagarumar gudunmuwar da Mangal ya bayar domin tabbatar da samun canji a lokacin za6en da ya gabata.

Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa mai girma shugaban kasa Muhammad Buhari ya yaba da irin kokarin Mangal don haka ne ya kara ma shi girma daga mukamin GOC ya koma “ Field Marshal” na siyasa.

A cewar gwamnan na jihar Katsina mai girma shugaban kasa Muhammad Buhari yayi la’akari da cewa shi “GOC” na kula da wani yanki ne kawai. Shi kau Field Marshal na kasa ne baki daya. Don haka siyasar Mangal ta wuce yanki , sai dai kasa baki daya,  don haka Mangal ya cancanci zama Field Marshal na siyasar Nijariya.

Hausawa na cewa “ a dade ana yi sai gaskiya “ wannan magana tabbas domin  da babu gaskiya a cikin al’amurran Alhaji Dahiru Mangal da tuni an wuce da yayinshi. Masoya Alhaji Dahiru Mangal na yi ma shi kirari da “ Mangal ikon Allah “. Tabbas wannan kirari yayi daidai da rayuwar Mangal domin al’amurran Mangal ikon Allah ne tilas sai kallo.

Dikko Bala K/Sauri,

Kofar-Sauri, Katsina.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!