Connect with us

LABARAI

Boko Haram Sun Kashe Sojoji 8 Wasu Sun Bata A Harin Buni Gari

Published

on

Rundunar sojojin Nijeriya ta tabbatar cewa mayakan Boko Haram sun kashe sojojin ta guda takwas (8) a harin barikin sojojin Buni Gari, a jihar Yobe, kamar yadda rundunar ta tabbatarwa wakilin mu.

Har wa yau kuma, ta bayyana cewa har yanzu akwai wasu sojojin ta wadanda suka yi batan-dabo a lokacin kai wannan harin.

Rundunar ta bayyana cewa, da farko ta gano gawar sojoji 6, a ranar Lahadi, daga bisani kuma ta sake gano karin gawar wasu sojojin guda biyu (litinin), wanda ya bayar da jimlar sojoji takwas (8) da suka mutu a wannan harin. Inda har yanzu akwai wasu sojojin da bamu san inda suke ba (MIA).

A hannu guda kuma, wata majiya daga babbar asibitin kwararru- General Sani Abacha Specialist Hospital, Damaturu, ta tabbatarwa Leadership A Yau cewa an kawo gawawakin sojoji guda takwas a asibitin.

Tare da fayyace cewa, an kai gawar sojoji 6 a asibitin, ranar Lahadi, kana kuma aka kawo saura biyun daga bisani.

A gefe guda kuma, mayakan sun kona barikin sojojin dake garin Buni Gari tare da kona ta sakatariyar jam’iyyar APC da ke garin- kurmus.

Buni Gari, yana karkashin karamar hukumar Gujba, a jihar Yobe, yankin da ya sha fuskantar hare-haren mayakan. Haka zalika kuma, a yan kwanakin nan, an kaiwa barikin sojoji na Buni Gari, sau- biyu: na ranar 7 ga watan Nuwamba a Katarko, da na 27 ga watan.

A hannu guda kuma, bayan kai wannan harin, kwamandan yanki na 2, a rundunar Lafiya Dole, Birgediya Janar Mohammed Baba Dala, ya kai ziyarar gani da ido a garin Buni Gari- dangane da yanayin harin.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!