Connect with us

KASUWANCI

Gwamnatin Tarayya Ta Samu Gibin Naira Tiriliya 1.1 A Kasafin Kudin 2018 Cikin Wata 6

Published

on

Ofishin Kasafin Kudi na Tarayya ya bayyana cewa daga watan Janairu zuwa watan Agustar shekarar 2018, kasafin kudi na tarayya ya samu naira tiriliyan 1.14 na gudanar da ayyukan gwamnatin. Kasafin kudi na shekarar 2018 da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattabawa hannu, an kashe jimlarnaira tiriliyan 9.1 da suka hada da , kudin manyan ayyuka har naira tiriliyan 2.87 dakuma kudin ayyukan yau da kullum da suka kai yawan naira tiriliyan N3.51 wanda babu bashi a ciki, sai kuma ayyukan da ake son yi dake da naira tiriliyan 2.01. Naira tiriliyan 9.1 ta kasafin kudin, ana sa ran za’a samar dasu daga cikin naira tirilyan 2.99 daza’a samu daga kudin harajin mai, sai naira biliyan 31.25 da za’a samar daga fannin iskar, indakumanaira biliyan 1.17 ake sa ran tarawa daga kudin shigar fannin ma’adanai. Don a zubawa kasfin kudi, Gwamnatin Trayya ta kammala shirin tara naira biliyan 658.55 daga harajin kamfanoni da ya kai naira biliyan 207.51 na harajin BAT da kuma naira biliyan 324.86 daga hukumar hana fasa kwauri ta kasa da ake sa ran samun nairabiliyan 57.87. har ila yau, ana sa ran Gwamnatin zata tara naira biliyan 847.95 ta hanyar tara haraji daga hukumomin ta, inda kuma, aka samu wani harajin a shekaraun baya da aka samar daya kai naira biliyan 87.84, naira biliyan114.3 da kuma naira biliyan 250. Bugu da kari, cikakkun bayanai na kokarin da kasafin kudi na shekarar 2018 da aka sanya a cikin kasafinkudin shekarar 2019 a karshen watan Agusta hakikanin harajin na Gwamnatin Tarayya a cikin watan Agusta ya kai yawan naira tiliyan 2.48. A cikin takardar ta kasafin kudin da Ministan tsare-tsaren kasa Sanata ya sanyawa hannu Udo Udoma ya ce, hakikanin naira tiriliyan 2.48 na kudin haraji, kimanin 52 bis adari sun kai naira tiriliyan 4.78 na kasafin kudi. An kuma danganta faduwar data kai kashi 48 bisa dari na kokarin da aka yi a fannin harajin mai da kuma fannin da baidanasaba da mai. Sakamakon jinkirin daaka samu na wanzar da harajin kadarorin mai da kuma kokarin da kamfanonin Gwmanatin Tarayya take yi, hakan ya kara nuna yadda fannin da bai shafi mai ba aka samu faduwar samun haraji. A bisa abinda aka kashe jimmlar ta kai naira tiriliyan
9.12, an kuma kashe naira tirilyan 3.64 daga watan Janairu da watan Agusta. Acewar kundin, hakan ya nuna an samu faduwa ta kimanin nira tiriliyan 2.44 sama da yadda aka sa ran kashewa na sama da naira tiriliyan 6.08 a cikin watan Janairu zuwa watan Agusta. A bisa fashin bakin da aka yi ya nuna cewar, an samu jimlar naira tiriliyan3.64, inda takai jimlranaira tiriliyan1.83 daaka sakarwa fannin ayyukan yau da kullum don biyan albashi, kudin fansho da sauran ayyukan yau da kullum. Acewar kundin, abinda aka fitar na ayyukan yau da kullum bayan kasafin kudin na 2018 an rabbata hannu sun zama doka a ranar 20 ga watan Yunin 2018. Ragin da aka samu ya shafi biyan albashi da biyan bashi manyan ayyuka. An samu jimlar naira biliyan 486.29 da aka fitar a ranar 17 ga watan Okutobar shekarar 2018. A hakikanin gaskiya, gibin 1.14 a cikin watan Agustar shekarar 2018, wanda ya kai kimanin kashi 58 bisa dari na gibin a daukacin shekekrar. Har ila yau, kundin ya ce, na fitar da naira tirilyan 1.54 don a ciki gibin bashi a cikin watanni takwas da suka wuce. A karshe kundin ya ce, a fitar da naira tiriliyan 3.64 a cikin wata takwas,indaaka cire naira biliyan 486.29 da aka turawa hukumomin gwamnati a a ranar 17 ga watan Oktoba don gudanar da manyan ayyuka.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!