Connect with us

MANYAN LABARAI

Mafi Karancin Albashi Ne Zai Tantance Yadda Za Mu Kada Kuri’a A Zaben 2019 –Kungiyar Kwadago

Published

on

Karin ko rashin karin mafi karancin albashi shine abinda ‘yan kungiyar kwadago zasu yi amfani da shi wajen kada kuri’a a zabukkan shekarar 2019 da muke fuskanta, wadannan sune kalaman da sakatare-janar na kungiyar ya furta a yayin da ya gana da manema labarai yau Laraba a garin Abuja.

Dakta Peter Ozo-Eson, ya fadin hakan ne bayan la’akari da tsaiko da aka samu wajen amincewa da karin mafi karancin albashin da shugaban kasa Buhari ya yi, ‘yan kungiyar sun bukaci shugaban kasan ya gaggauta mikawa majalisun tarayya amincewar ta shi don su sanya mafi karancin albashin a matsayin doka.

‘In har ba a aiwatar da mafi karancin albashin ba, za mu yi amfani da shi wajen tantance wa zamu kada wa kuri’a ko wanene ba zamu zaba ba a zaben shekarar 2019, yakamata gwamnati ta yi gaggawar aiwatar da mafi karancin albashin kafin lokacin zabukkan su gabato, saboda kada su cakuda da batun zabukkan.’ Inji Eze-Eson

Yanzu kimanin kusan wata guda kenan da kwamitin ‘yan uku karkashin jagorancin Ama Pepple ya mika rahoton shi ga shugaban kasa Buharin, inda kwamitin ya bukaci gwamnatin tarayya ta amince da Naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi daga watan Oktoban da ya wuce, amma har yanzu shuru ba a ce komai ba game da batun.

Kungiyar kwadagon ta bukaci mambobinta da al’umma gaba daya da su yi amfani da wannan damar wajen korar wadanda basa goyon bayan mafi karancin albashi daga mukamai, saboda ma’aikatan kasar nan sun dade da cancantar wannan karin, amma ‘yan siyasa marasa tausayi da kishi sunki amincewa da karin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!