Connect with us

RAHOTANNI

Ta Hanyar Kulla Aure Tsakanin Masu Cutar Kanjamau Ya Sa An Samu Raguwar Yaduwarsa A Bauchi (I) -Usman Ziko

Published

on

USMAN ABUBUKAR ZIKO, Shi ne shugaban masu dauke da cutar nan mai karya garkuwar jiki wato (KANJAMAU) a jihar Bauchi. Kasantuwar a ranar Asabar 1, ga waran Disambar nan ne majalisar dinkin duniya ta ware domin tunawa da cutar KANJAMAU. A bisa haka wakilinmu KHALID IDRIS DOYA ya tattauna da shi kan cutar da kuma hanyoyin da ake bi domin rage mata karfi a jihar Bauchi. Sun tabo batutuwa da dama asha karatu lafiya:

Ka bayyana kanka ga mai karatu mana?
Sunana Usman Abubakar Ziko, nine shugaban masu dauke da cutar nan mai karya garkuwar jiki wato KANJAMAU na jihar Bauchi gabaki daya.

A wace marhala masu dauke da wannan cutar suke yanzu haka a jihar Bauchi?
Gaskiya ana samun ci gaba matuka gaya a sakamakon goyon baya da kuma janyo mu a jika da ake yi a jihar nan. a bisa kokarin yakar yaduwa da cutar, a cikin hukumar da ke sanya ido kan yaki da wannan cutar wato BACATMA mu ‘yan jihar Bauchi da muke dauke da wannan cutar mu 10 muke aiki a cikin hukumar, wannan ya basu damar bayar da hadin kai gaya wajen rage yaduwar cutar. Sanna, a gefe guda kuma ana samun ci gaba musamman ta fuskacin hada aurtayya da daukan nauyin auren da wannan hukumar ta BACATMA ke yi, a bisa haka ne take samun damar daura dukkanin jama’an da suke dauke da wannan cutar kan turbar da ta dace, don haka ne ake samun raguwar haifar yara masu dauke da cutar. A baya-bayan nan, hukumar BACATMA ta biya wa masu dauke da cutar KANJAMAU su 179 kudin sadaki da hidimar aurensu (maza da mata kenan), a cikin wannan auren, an samu haihuwar jarirai 72 cikin yardar Allah yaran nan basu dauke da cutar KANJAMAU, alhali iyayensu suna daure da cutar, ka ga wannan taimakon shirin tallafin ne, domin idan hukumar ce ta hada auren, tana kokarin bayar da shawarori da kuma daura ma’aurata kan hanyoyin da zasu domin domin kada yaransu su kamu da cutar. Don haka muna rokon hukumar BACATMA ta daura da kara himma domin wannan tallafin aurer da masu dauke da cutar na taimaka gaya.

To yanzu wasu kalubalen ne ku ke fuskanta a halin yanzu musamman a jihar Bauchi?
Matsalolin da muke fuskantan dai yanzu ba su wuce na kyama da tsangwama daga mutanen da basu kammala wayewa ba sosai. Amma yanzu an fi samun irin wadannan matsalolin ne a kauyuka musamman wadanda ba su gama waye ba; sune suke nuna kyama da kuma tsangwama ga mutane masu sauke da wannan cutar na KANJAMAU, ana nuna wa mutanenmu masu dauke da wannan cutar kyama sosai a kauyuka. Amma a cikin gari abun ba sosai ba, nuna kyamar nan gaskiya yana jefa masu dauke da cutar nan cikin damuwa sosai, domin wasu za suke boyewa har ta kai sun samu lalura sosai wanda in ba a yi sa’a ba za iya kaisu ga hallaka.
Sannan kalubalen da yanzu haka muke fuskanta na biyu shi ne rashin abun yi ga mambobinmu musamman mataye. Macece za ka sameta tana dauke da wannan cutar, mijinta shi ma na dauke da wannan cutar ya kuma rasu ya barta da yara biyu ko uku wasu ma fiye har zuwa goma ana samu. A cikin yaran nan ba za a rasa biyu ko daya mai dauke da kwayar wannan cutar na KANJAMAU ba. ka ga ke nan uwa tana shan magani, ‘ya’yanta suna shan magani. Matsalar da muke fuskanta a nan shi ne babu sa’ana wanda zai dauke wa matayen nan dawainiyar yaransu musamman ta fuskacin abinci, ka san shi wannan cutar na matukar bukatar abinci mai gina jiki a kowani lokaci. Mafiya yawan mataye masu dauke da wannan cutar babu makaranta, babu abun yi, babu aikin gwamnati, kai yadda ma za ta yi ta je domin karbar magani a asibiti babu hali. matsarar rashin abun yi na juyawa ga matayenmu yana matukar daga mana hankali sosai.

Akwai wani abun da kake son jama’a su maida hankali a kai musamman kan matsalar da ya shafi ku masu dauke da wannan cutar?
Lallai akwai tabbas mazanmu kai har ma da matayenmu akwai abubuwan da wasu suke yi wanda bai kamata ba; kuma wajibi ne mu bayyana wa jama’a domin su kula su kuma lura sosai. Wasu mazajenmu sukan rinka boye wannan cutar nasu, hatta ma wajen da suke zuwa asibiti domin amsar magani sai suke zuwa wani waje don kar a gansu a san suna dauke da KANJAMAU, irin sune suke zuwa wani wajen na daban inda ba a sansu ba sai su ba da kudade masu yawa domin su biya sadakin wata yarinya su auresu, mafiya yawan masu irin wannan halin sukan nemi yara kanana suna aurensu sai su je su sanya musu irin wannan cutar ta KANJAMAU wanda haka ke kara cutar da al’ummarmu gaya. Muna samun irin wannan matsalar sosai, don haka ne muke kira ga jama’a da babbar murya don Allah don Annabi ake yin gwaji kafin aure. Saboda shi wannan cutar bai nunawa a jiki ko a fuska, ko ka shekara dari kana shan maganin wannan cutar idan aka zo aka gwada za a samu akwai saboda haka ake yin gwaji kafin aure. Ina sake nanatawa jama’a su sanya wannan a ransu, matukar aka dauki wannan da muhimmanci to za a samu raguwar kamuwa da wannan cutar a tsakanin al’umma. Haka su ma matayenmu akwai masu boye wannan cutar suna auren wasu mazaje wannan kuma baya haifar da komai sai karuwar mambobinmu ma’ana masu dauke da wannan cutar alhali hakan ba ci gaba bane.

Me za ka je ga masu dauke da wannan cutar ganin cewar su tsaya auren wadanda sun san basu dauke da wannan cutar?
Masu dauke da wannan cutar KANJAMAU dole mu kasance masu jin tsoron Allah mu dauka jarabawace a garemu. Kullum abun da muke fada ke nan, malamai su ma suna fada dukkaninmu masu dauke da cutar KANJAMAU su sani jarabawace Allah ya jarabce su da shi, matukar mutum ya tsaya kan matsayarsa ya ji tsoron Allah zai samu rayuwar da sauki. Ana aure a tsakanin masu dauke da wannan cutar har su yi aure su kuma haifi yaron da bai dauke da wannan cutar ta hanyar da ake bi na (PMTCT) mai dauke da wannan cutar da mace mai dauke da wannan cutar su kan yi aure su kuma haihu yaran da ba su dauke da wannan cutar, an yi hakan sosai mun gani don haka ya kamata dukkanin mai dauke da wannan cutar ya je ya nemi mace mai dauke da irin wannan cutar domin su kulla sosayya domin shi ne mafita ga kasarmu da al’ummarmu ba wai mutum ya je yana auren wanda bata dauke da wannan cutar ba. kamar dai yadda na bayyana maka a farko kan yadda BACATMA ta yi kuma an samu natijarsa.

Ta yaya ku ke kulla wannan auren a tsakanin mambobiinku?
Mafiya yawa masu dauke da wannan cutar sun fi haduwa a asibiti a wajen amsar magani ko gwaji, ka san amsar maganin masu dauke da wannan cutar na musamman ne a bisa haka sai ka ga wasu har sun fahimci junansu. Alhamdullahi, mu sai godiya domin hukumar BACATMA tana ba da tallafin auren nan. Idan mutane mace da na miji suka hadu a wajen karbar magani suka daidaita tsakaninsu kan maganar aure, sai su rubuta wasika wa hukumar BACATMA ita kuma tana ba da tallafin auren nan. Yanzu haka an baiwa mutane kusan 179 kudin sadaki a jihar Bauchi. daga shekaru biyar zuwa yau an baiwa masu dauke da wanna cutar tallafin kudin sadaki sama da mutane dari da saba’in ta hanun wannan hukumar.

Mafiya yawa daga cikin wadannan mutanen da aka ba su wannan tallafin sun yi auren nan kuma ‘ya’yan da suka haifa ba su kamu da wannan cutar ba. don haka na ke kira ga masu dauke da wannan cutar da su ji tsoron Allah. Mutum ya sani Allah ne ya daura masa wannan cutar ya gani shi za ka fi karfin zuciyarka ka rike kanka ko yaya. Idan kuma mutum ya ki ya rike wannan kaddarar Allah zai iya kamasa ta wani hanyar kuma wanda kai kanka ba za ka ji dadinsa. Ina kira ga ‘yan uwa maza da mata da mu ji tsoron Allah mu rinka kulla auratayya a tsakaninmu. Ni abun takaicin ma shi ne yau mutum bai nemi wacce take dauke da wannan cutar domin ya aure ya rasa ba; mace bata nemi mai irin wanna cutar domin ta aura ta rasa ba don mene ne mutum zai je yana boye wannan cutar har ya auri wata ya je ya shafa mata wannan cutar? Mutum bai da wani dalili amma su kansu al’umma dole suke kura domin rage yaitar kamuwa da cutar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: