Connect with us

MANYAN LABARAI

Yaki Da ’Yan Bindiga: Sarakunan Zamfara Sun Nemi A Ba Su Bindigogi

Published

on

Sarkin Anka kuma shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad, ya bukaci gwamnatin tarayya ta samar musu da manyan bindigogi samfurin AK 47 da sauran kayan yaki don su fattataki ‘yan ta’addan dake kashe kashen mutane tare da garkuwa dasu a fadin jihar.

Sarkin ya mika wannan bukata ne a yayin bikin raba mashina 850 ga sabbin ‘yan kato da gora da a ka dauka kwanan nan a jihar don tallafa wa wajen kawo karshen harkokin ‘yan ta’adda a jihar.

Ya kara da cewa, ‘yan ta’addan na amfani da bindiga kirar AK 47 ne wajen sace sacen shanaye da garkuwa da mutane a jihar a saboda haka ya kamata a samar wa da mutane irin wadannan makaman don su fuskanci ‘yan ta’addan gaba da gaba.

“Lallai muna cikin matsala, al’amurra na kara lallacewa a kullum, ‘yan ta’addan na kara canza salo saboda haka dole gwamnatin ita ma ta canza salo, ya kamata a tabbatar da tura jami’an tsaro a dukkan inda ake da tsammanin faruwar ayyukan ta’addanci a jihar,” inji shi.

Barasaken gargajiyar ya kuma bayyana cewa, mutanen jihar na cikin tashin hankali duk da jam’an tsaron a aka baza a fadin jihar, ‘yan ta’adda na ci gaba da harkokinsu na cin zarafin jama’a babu kakkautawa a fadin jihar.

“Noma da kiwo ne babban sana’ar mutanen jihar kafin wannan lokacin amma a halin yanzu mutane da yawa sun gudu sun bar harkar noma, ‘yan ta’adda sun mamaye fadin jihar,” inji shi

Sarkin ya kuma roki jama’a jihar da su daina biyan kudin diyya in ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da dan uwansu, domin kuwa duk wanda ya mutu a hannun ‘yan ta’addan ya mutu a matsayin shahidi.

A nasa jawabin, kwamishinan kananan hukumomi da masarautun gargajiya, Alhaji Bello Dankande Gamji, ya ce, dokokin kasa ya yi cikakken bayanin wanda yake da hurumin daukar bindiga, ya kuma mika godiyarsa ga sarakunan gargajiya a bisa kokarinsu na samar da zaman lafiya a fadin jihar.

Ya ce, sun fahinci cewa, duk yawan jami’an  tsaron da aka samar a jihar in har ba a hada da ‘yan sintiri ba, samun nasarar zai yi wuya, saboda sune suka san ‘yan ta’addan da kuma lungunan da suke boye cikin jihar gaba daya.

“Duk da barazanar mutuwa da nake samu, bazan daina aikin dana sa a gaba ba, inji shi, ana sa ran fara biyan ‘yan sintirin wasu kudade da duk wata daga wannan mako don kara karfafa su ci gaba da gudanar da ayyukansu,” inji shi.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!