Connect with us

SIYASA

2019: Atiku Zai Ga Jama’an Da Suka Fi Na Sakkwato Idan Ya Zo Nasarawa –Kungiyar Mata

Published

on

Kungiyar Mata zalla na Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa, sun kaddamar da gangamin yakin neman zaben Atiku da Peter Obi a fadin Jihar baki-daya.
A ranar Laraba ne Shugabannin kungiyar Mata zalla na Jam’iyyar PDP suka gudanar da taron membobin kungiyar a zauren taro na Jam’iyyar PDP da ke garin Lafia.
Da take zantawa da manema labarai, Shugabar kungiyar Mata zalla na yakin neman zaben Atiku Abubakar, da Peter Obi, a Jihar Nasarawa, Hajiya Harira Ibrahim ta ce; yau Allah ya kawo mu lokaci ya yi da za mu fito kwai da kwarkwata wajen kira ga Mata da su fito kwai da kwarkwata su zabi Atiku Abubakar da Peter Obi, a matsayin wadanda za su Mulki kasan nan a zabe mai zuwa.
Hajiya Harira Ibrahim ta ce; wannan zaman da muke yi yau muna yi ne domin kara damara a fadin Jihar. Shi ya sa muka kara kiran taron Shugabannin Mata na yakin neman zaben Atiku da Obi a 2019. Ta kara da cewa, Mata su ne kashin bayan siyasa, saboda duk kuri’u masu yawa daga mata ne suke fitowa, duk da cewa mata suna korafi cewa suna shan wahala a wajen zabe amma ba su moruwa daga ribar Dimokuradiyya.
Hajiya Harira Ibrahim ta ce; dole mu kara wayar da kan mata su tashi tsaye su fito su marawa PDP da Atiku Abubakar baya, saboda ta tabbata Atiku mutum ne mai tausayi kuma yana taimakawa marasa galihu. Ta kara da cewa, a kwanaki mun karanta a jaridu dubban matan da Atiku ya ba su aiki a kamfanin shi. Kuma ya kara albashin ma’aikatan kamfanin shi. Ta ce: wadanda ba su san waye Atiku Abubakar ba ne suke sukar shi. Kowa yasan irin rawar da Atiku ya taka wajen taimakawa al’umma musamman ‘yan Arewa lokacin yana Mataimakin Shugaban kasa.
Hajiya Harira Ibrahim ta ce; yanzu mata za su san sun yi zaben gaskiya, saboda siyasa ce wanda babu muna-muna za a zabi mutumin da zai ceto mu daga wahala da yunwa da talauci, zai samar da zaman Lafiya na gaskiya da gaskiya ba na farfaganda a jaridu ba.
Ita ma da take jawabi, Mataimakiyar Shugaban kungiyar Matan, Ruth O.K.K. ta ce; wannan rantsattsiyar kungiyar mata na Jam’iyyar PDP masoya Atiku da Obi ta yi alkawari cewa; jama’an da aka gani a Sakkwato kadan ne a kan wanda za su taru a Jihar Nasarawa.
Ta ce; idan lokaci ya yi, tawagar PDP ta yi yekuwar zuwa gangamin yakin neman zaben Atiku a Jihar Nasarawa, za a ga milyoyin jama’a da yardan Allah. Ta ce; muna da mutane da yawa mata masu fada a ji, wadanda suke APC a nan Jihar sun sanar da mu suna tare da mu a wannan tafiyar, amma ba za su bayyana kansu ba, saboda suna rike da mukamai a APC amma idan lokaci ya yi za su bayyanar da kansu.
Ta kara da cewa; Jihar Nasarawa Jiha ce ta Jam’iyyar PDP, saboda babu wata Jam’iyyar da ta taba cin zabe a Jihar Nasarawa bayan PDP. Ko lokacin da Buhari yake da farin jini bai iya cin zabe a Nasarawa ba, bare yanzu da jama’a ke cikin tsananin wahala na yunwa da talauci da
ya tsunduma su. Ta ce; idan Allah Ya yarda, PDP za su ga yawan kuri’a da za a kada masu a Jihar Nasarawa a 2019.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!