Connect with us

LABARAI

Aisha Buhari Ga Matan APC: Ku Ilimantar Da ’Yan Nijeriya Kan Nasarorin Buhari

Published

on

Uwargidan Shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bukaci reshen mata na Jam’iyyar APC da su rika wayar da kan ‘yan Nijeriya a kan irin nasarorin da gwamnatin Shugaba Buhari ta samu.
Aisha Buhari, ta yi wannan kiran ne a wajen taron sashen matan Jam’iyyar na APC, mai taken 4+4 2018 a Abuja, ranar Talata.
Shi wannan shirin na, 4+4 Buhari/Osinbajo 2019, magoya bayan Buhari da Osinbajo ne suka kirkiro shi, domin tabbatar da ganin an sake zaban na su su biyu a babban zabe na 2019.
“Ina kuma yin kira a gare ku da ku rika wayar da kan al’umma a kan manufofin Jam’iyyar mu, wanda ta yi alkawarin canja yanayin rayuwar kuncin da ‘yan Nijeriya suke ciki, da kuma irin kokarin da gwamnatin ta yi a halin yanzun.
Ta yi kira ga matan da kar su gajiya a kan kokarin da suke yi na ganin sun wayar da kan mata wajen tabbatar da samun nasarar Jam’iyyar a babban zaben 2019.
Uwargidan ta Buhari ta ce, da fara yakin neman zaben na 2019, babban abin da ke gaban matan Jam’iyyar ta APC shi ne yada mahimman bayanai, wayar da kai a kan harkokin da suka shafi tsaro, da kuma yin gargadin siyar da kuri’u.
Daga nan sai uwargidan Shugaban kasan ta janyo hankulan matan da aka zabo su daga dukkanin kananan hukumomin kasar nan 774 da su bayyana wa Duniya irin nasarorin da gwamnatin ta Buhari ta samu.
A nata jawabin, Uwargidan mataimakin Shugaban kasa, Dolapo Osinbajo, cewa ta yi, gwamnatin APC ta yi namijin kokari wajen yaki da ta’addanci da kuma sake ginawa da farfado da al’umman yankin da ta’addancin ya daidaita.
A jawabin ta, babbar mai taimaka wa Shugaban kasa, Dakta Hajo Sani, ta bukaci matan ne da kar su gajiya a kokarin da suke yi na tabbatar da an sake zaban Shugaba Buhari da Osinbajo, a babban zaben 2019.
A cewar ta, mata sun gamsu da cewa gwamnatin Buhari ta kammala tare da kagan wasu sabbin hanyoyin mota da kuma samar da manyan ayyukan raya kasa da kuma bunkasa dukkanin sassan kasar nan.
Hajo Sani, ta yaba da kokarin da Uwargidan Shugaban kasan ke yi na inganta rayuwar mata da yaran kasar nan ta hanyar samar da daidaito tsakanin maza da mata a Nijeriya.
Ita ma tsohuwar mataimakiyar Gwamnan Jihar Filato, Pauline Tallen, kira ta yi ga matan na Nijeriya da su goyi bayan takaran na Buhari da Osinbajo, a babban zaben na 2019, domin cin gajiyar nasarorin da aka samu.
Tun da farko, Shugabar matar Jam’iyyar ta APC, Hajiya Salamatu Baiwa, ta bukaci matan Jam’iyyan ta APC ne da su guji yin kamfen da karya ko bata sunan wani.
A cewar ta, Jam’iyyar APC ta taka rawar gani, musamman wajen samar da manyan ayyukan raya kasa, fada da ta’addanci, yaki da cin hanci da karban rashawa da kuma shirye-shiryen ta na bayar da tallafi.
Don haka, sai ta yi kira ga matan Jam’iyyar ta APC da su yi yakin neman zaben su ne da bayyana nasarorin Jam’iyyar a dukkanin tarukan su kafin zaben na 2019.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: