Connect with us

SIYASA

Al’ummar Arewa Maso Yamma Sun Nuna Goyon Baya Ga Atiku —Najeeb Kura

Published

on

Ko’odineta na kungiyar “Fully and truelly Atikulated” Kwamared Najeeb Nasir Kura ya bayyana cewa kaddamar da takarar shugabancin kasa da Atiku Abubakar ya yi na jihohin Arewa maso yamma a garin Sakkwato ya nuna al’ummar Arewa sun amsa kira sun nuna yardarsu da takarar Atiku.
Ya yi nuni alamu sun nuna lokaci ya yi na Wazirin Adamawa ya zama Shugaban kasar Nijeriya alamu sun nuna kamar yadda ake cewa tun daga laraba juma’ar da za ta yi kyau take fara wa lokaci kawai suke jira a kada kuri’a ga takara Atiku.
Ya ce, ya kamata wanda ma bai zo an tafi da shi ba a wannan takara ya kamata ya zo a yi da shi domin akwai alamun nasara kararar a bayyane, domin Atiku Mutum ne wanda kowane yanki na kasar nan sun yarda mutumne wanda zai samarwa duk dan kasa mafita zai kuma kai kasar nan ga tudun muntsira ta kawo ayyuka na ci gaba da zai amfani al’ummarta.
Kwamared Najeed Nasir ya ce, a matsayinsu na matasa sun gamsu da tsare-tsaren Atiku ga matasa musamman ma da ya ce, zai bai wa matasa kashi 40 na tafiyar da Gwamnatinsa, wanda tun daga yanzu sun soma gani a kungiyarsu ta Atikulated da kusan duk matasa ne suke jagorancinta a yakin neman zabe da suke ga Atiku.
Jagoran na kungiyar Atikulated ya ja hankali al’umma musamma ma matasa su tsaya su jajirce su zabi Atiku a zabe mai zuwa dan shi ne zai kulada hakkinsu ya gina kasar ta yanda kowa zai sami walwala matasa su tsaya da kafafuwansu yanda za su sami dammar ba da cikakkiyar gudummuwa don ci gaban al’umma. Kungiyarsu ta Atikulated tana kai wa da kawowa ba dare ba rana birni da kauye sako da lunguna wajen wayar da kai kan anfanin zabar Atiku ya zama shugaban kasa a zabe mai zuwa na kasar nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: