Connect with us

LABARAI

An Sake Cafke Deji Adeyanju

Published

on

Bai wuce awa 24 ba da sakin dan rajin kare hakkin bil’adamar nan, kuma shugaban kungiyar ‘Concern Nijeriya’, kungiyar fafutukar samar da adalci a cikin al’amurran Nijeriya, wato Deji Adeyanju, an kuma sake mayar da shi gidan yarin Keffi a karo na biyu.
Alkalin kotun Majistare da ke Wuse II Abuja ne ya bayar da umurnin mayar da Dejin bayan sauraron tuhume-tuhumen da hukumar ‘yan sanda ta shigar a kan sa, tuhumar da ta hada da cin mutunci da bata sunayen wasu, zargin laifuka a kan wasu, da kuma aikata laifukan yanar gizo.
Alkalin kotun, Idiat Akanni ya daga sauraron shari’ar zuwa ranar Alhamis, in da za a saurari rokon yiyuwar bayar da Deji Adeyanju beli.
Wannan takun sakar da ke tsakanin dan karin rajin hakkin Bil’adam, Deji Adeyanju da hukumar ‘yan sanda ya samo asali ne a yayin da ya jagoranci zanga-zangar lumana a babban ofishin ‘yan sanda da ke Abuja bisa zargin jami’an tsaron na kasancewar su kayan aikin ‘yan siyasa, a maimakon ‘yan ba ruwanmu.
A karon farko a ranar, an kama shi ne tare da mutum biyu wadanda suke zanga-zangar tare; Daniel Abobama da Boma Williams, in da aka gabatar da su a kotun Majistare, Karshi, in da alkalin ya bada umurnin tsare su a gidan yarin Keffi, jihar Nasarawa.
A kamun farko, ana zargin su Deji ne da laifuka da suka hada da; makirci don aikata laifi, takurawa al’umma, da cinmutunci da bata suna, da zubar da kimar hukumomi, wanda yake ya saba wa dokar Nijeriya sashe na 96,113,114,152,183, da 391 na tsarin final kod.
Bayan da Alkali ya bada su beli, basu samu damar cika sharuddan ba, wanda ya hada da ma’aikaci mai matakin aiki na 14, tare da sa hannun ma’aikatarsa, da kuma dan kasuwa, wanda hakan ya jaza masu zama a gidan kason har zuwa ranar Litinin.
Bayan samun cika sharuddan belin ranar Litinin din, sauran mutum biyun Abobama da Williams sun samu fita, sai dai shi Adeyanju, a nan take ‘yan sandan suka sake kama sa a karo na biyu da wasu sababbin tuhume-tuhumen.
A yayin zanga-zangar da tayi sanadiyar kama sun, Adeyanju tare da sauran mutanen sa sun tafi ne da hotuna da banoni masu dauke da rubutu a harshen turanci: ‘Yan sanda ba ‘yan siyasa ba ne, wannan zanga-zangar tamu ta kiyaye Dimkoradiyar mu ce, Zaben 2019 na cikin Hadari’.
Masu zanga-zangar sun nuna damuwarsu kan abubuwan siyasa da ke faruwa a Nijeriya, na yanda, a cewar su, ‘yan sanda sun zama kayan aikin jam’iyar APC wurin murkushe duk wani da ake ganin dan adawar ta ne
Da yake bayani kan dalilin tsare su, kakakin rundunar ‘yan sanda, Jimoh Moshood ya bayyana cewar, su din sun taka doka ne. ya kara da cewar, laifukan da ake zargin su da aikatawa na cin mutunci da bata suna ka iya haddasa rikici, tashin hankali, da kuma cin zarafi da bata sunan hukumomi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!