Connect with us

KASUWANCI

An Samu Hauhawar Farashi Na Kashi 11.4 A Nijeriya – CBN

Published

on

Babban Bankin Kasa CBN ya sanar da crlewa, ana sa ran hauhawan farashi zai karu da kashi da kimanin kashi 11.4 bisa dari a cikin sauran a shekarar 2019. Gwnan Gwaman CBN, Godwin Emefiele ne ya sanar da hakan a jawabin sa a taron kasa na tsare-tsare na Nijeriya na shekarar 2019. Ya ce, hauhawan fashin ya na karuwa ne a bisa la’akari da tsimayin da ake yi na siyar durkushewa. Acewar rahoton kwanan baya da Hukumar Kididdiga ta Kasa ta fitar a cijin watan Okutobar shekarar 2018, ya ce, ga sauran shekarar 2018 da kuma tsakiyar shekarar 2019, hauhawan farashi a Nijeriya an auna zai kai karu da kimanin kashi 11.4 bisa dari sannan kuma ya daidaita daga baya.
Jaddawalin masu yin amfani da kayan masarufi da aka auna hauhawan farashin zata raguzuwa kashi 11.26 bisa dari a cikin ahekara daya na watan Okutobar shekarar 2018. Kididdigar ta sanar da cewa, wannan ya kai kashi 0.02 bisa dari kasa da yadda aka samu a watan Satumbar 2018 da ya kai kashi 11.28 bisa dari. Da yake tsokaci a kan kudin musaya ya ce, koda yake CBN ya yi kokarin kare martabar kudin na musaya, inda a yanzu wanda ake yin amfani dashi da ya fito daga kasuwa ake sa ran yaci gaba duk da matsin dake a kasuwar.
Ya ci gaba da cewa, matsin zai iya karauwa a lokacin zaben dake tafe, musamman ganin yaddda kasuwar ke kara yin turiri. Sai dai ya yi nuni da cewa, duk da wannan matsin CBN zai yi kokarin kare martabar da kudin musayar nan da yan watanni ma su zuwa. Ya ce, ana son in sanar cewar, samar da daidaito akan kudin na musayar wani abu ne da CBN ya sanya a gaba saboda mahimmanci da suke dashi. Akan sauran kasafi na biya kuwa Gidwin ya ce, ana sa ran zai kasance yadda yake na gajeren zango da kuma farashin mai da zai ci gaba da farfadowa.
A karshe ya ce, wannan zai samu tallafi daga bangaren da bai shafi fannin mai ba a bisa kokarin da ake yi na rage yawan shigowa dashi cikin kasar nan kuma CBN zai mayar da hankali wajen yin amfani da fasahar zamani don ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba, musamman fannin aikin noma.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: