Connect with us

MANYAN LABARAI

Arewa Masu Gabas Za A Tura Sabbin Jami’an Da Aka Kara Wa Girma –Buratai

Published

on

Babban hafsan sojin Nijeriya, laftanar janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa mafi yawa daga cikin jami’an da aka kara wa mukamai za a tura su arewa masu gabas ne, don karawa dakarun da suke a can din karfi, don ganin sun ci nasara a akan masu tada kayar baya a yankin.

Buratai din ya bayyana hakan ne a yayin da yake rantsar da jami’ai guda 29 zuwa mukamin manjo-janar, inda wasu daga cikin jami’an aka kara musu mukami zuwa birgediya janar, anyi karamin mukamin ne a yau Alhamis a birnin tarayya Abuja.

‘Wasu daga cikin wadanda aka ma karin girma a yau daga gobe zasu tattara komatsan su, su kama hanyar arewa masu gabas, baku da wani uzuri, daga nan sai arewa masu gabas ba tare da wani bata lokaci ba, an fitar da sunan jami’an da za a tura arewa masu gabas din, kuma zamu karanta jerin sunayen gareku a nan.’ Inji Buratai

Buratai din ya bukaci iyalin jami’an da za a tura yankin arewa masu gabas da su dauki aikin kula da iyalinsu, a yayin da mazajensu zasu ta fi kare martabar kasarsu, sannan su sani mazajen nasu juramai ne da suka cancanci wannan karin girman.

Buratai ya kara da cewa: Karin girman abu ne da ya cancanta sosai, sannan ku tabbatar kun kiyaye dokokin kasa da na aikin soji, ku dake ko jajjirce, ku zama jami’ai na kwarai wadanda zasu siya wa rundunar sojin Nijeriya mutumci a idon duniya.

An kara wa masu mukamin biregideya janar 29 zuwa mukamin manjo janar, masu mukamin kanal 95, zuwa mukamin birgediya janar, masu mukamin laftanar kanar 106 zuwa mukamin kanal, sai mai mukamin manjo daya da aka kara wa mukami zuwa laftanar kanal.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!