Connect with us

MANYAN LABARAI

Hatsarin Mota: Fayose Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Legas

Published

on

A ranar Laraba ne, hatsarin mota ta rutsa da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, a kan babban gadar ‘Third Mainland Bridge’ a jihar Legas.
Jami’in watsa labaran gwamnan, Lere Olayinka, ya tabbatar da haka a sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce, Fayose na karbar magani a wani asibiti bayan hatsarin.
Ya ci gaba da cewa, “Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Fayose ya samu hatsarin mota a kan babbar gana nan ta ‘3rd Mainland Bridge’ a Legas, ‘yan mintoci da suka wuce, a halin yanzu yana karbar magani a asibiti, kuma jikinsa da sauki kwarai da gaske.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!