Connect with us

SIYASA

‘Jam’iyyar AAC Alhairi Ce Ga Nijeriya’

Published

on

An bayyana cewa, a halin da ake cikin yanzu da kasar nan ke fuskantar rikice rikicen tattalin arziki nada tsaro, jam’iyyar AAC ce kadai za ta iya kawo wa kasar nan cikakken ci gaban da ake bukata, mataimakin dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar AAC, Dakta Rabiu Ahmad, a wata sanarwa da
Dakta Ahmad ya kuma kara da cewa, jam’iyyarsu ta AAC ta yi tanadin ayyukan alhairi don kyautata rayuwar jama’ar Nijeriya, ya yi wannan bayanan ne a sanarwa da ya raba wa manema labarai a garin Abuja ranar Talata da ta gabata.
Dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasar, ya kuma ci gaba cewa, “Abu na biyu, inaso nayi amfani da wannan dama na isar da sako a gare ku game da takara da zamuyi a jam’iyyar African Action Congress (AAC).”
“Abu na uku kuma, in tabbatar cewa bazamu taba yin kasa a gwiwa ba. Zamu dage mu tabbatar duk abinda kukeso ayi muku a gomnati, munzo mun saurare ku, kuma mun gabatar dasu yadda ya kamata.
Sunana Dr. Rabiu Ahmad Rufa’i, an haifeni ne a garin Ringim na jihar Jigawa. Na taso ni ba dan kowa bane, nazo nayi makaranta har Allah yasa nazo na zama likita. Na sadaukar da kaina gurin nemawa mutane lafiya da koyarwa a gurabe daban-daban. Wannan ne yasa da lokaci yazo aka bani dama na zamo abokin takara na Omoyele Sowore a karkashin jam’iyyar African Action Congress (AAC), saboda zabe mai zuwa na 2019.”
Ina so na tabbatar wa mutane cewa, lokaci ya yi da ya kamata mu tsaya mu natsu, mu gano cewa wasu daga cikin yan siyasa na wannan kasa (Nijeriya) da suka samu dukiyar al’umma suka yi fata-fata da ita tare da cika aljihunansu da kudaden mu, sune suke dawo wa duk lokacin da aka ce zabe ya zo ya bamu Naira dari biyu (N200) domin mu zabe su.”
“Ina so na tabbatar wa mutane cewa, wannan lokacin baza ayi haka ba. Muna so mutane su tsaya su zabi mutane masu nagarta, masu inganci, wanda suka san me suke yi, wadanda za su kawo musu karshen wahalar da suke sha, ta hanyar bunkasa tattalin arziki da ilimi da lafiya da gina tituna da gina dam-dam nayin noma da bayar da taki da tsaro na dukiya da lafiya. Da kuma bawa mutane hurumi na suyi kokari su fitar da kansu daga kangin talauci.”
“Ba za mu taba yin kasa a gwiwa ba, muna nan muna yawo babu birni ba kauye, ba dare ba rana muna sauraron ku. Muna so daku damu mu hadu mu fitar da kanmu daga cikin wannan halin da muke ciki.
Lokaci ya yi, saboda haka, wannan shi ne karo na farko da nake isar da wannan sako. Amma mu tara a gaba, bi izinillahi zan ci gaba da kawo sakonni irin wannan. Kuma kullum za mu tsaya muna sauraronku don mu share muku hawaye. Muna kara godiya. Allah ya muku albarka, Allah ya yi wa kasar mu Nijeriya albarka”.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!