Connect with us

SIYASA

Jam’iyyar SDP Ce Kadai Za Ta Ceto Al’ummar Jigawa Daga Kuncin APC –Jumbo

Published

on

Dan takarar gwamnan jihar Jigawa karkashin tutar jam’iyyar adawa ta SDP Alhaji Bashir Adamu Jumbo ya ce jam’iyyarsa ta SDP ce kadai mafuta daga kuncin da jam’iyya mai mulki ta APC ta jefa al’ummar wannan kasa.
Jumbo ya yi wannan furuci ne, a ya yin zantawarsa da ma nema labarai jim-kadan bayan kammala tattaunawar shuwagabannin jam’iyyar da ‘yan takarkaru wadda aka gudanar a birnin jihar dake Dutse.
Dan takarar wadda ya zargi jam’iyya mai mulki bisa yunkurin yin amfani da kudi domin yaudarar talakawa a zabe mai zuwa, ya ce babu ko shakka jam’iyya mai mulki ta APC za ta zama tarihi a jihar bayan kammala zaben na 2019 mai zuwa.
‎”Ko tantama babu duba da irin dumbin al’ummar da suka halarci taronmu da muka gudanar a garin Bulangu wannan manuniya ce ta cewa al’ummar jihar Jigawa sun gaji da kuncin mulkin jam’iyyar APC kuma sun rungumi jam’iyyar SDP a matsayin mafuta” inji Jumbo.
Haka kuma a cewarsa, gwamnatin APC a jihar ta gaza cimma alkawurr‎an da ta daukarwa al’ummar jihar a lokacin kamfen din shekarar 2015 illa kawai yaudara da fakewa da tabarbarewar tattalin arziki.
Sannan ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su guji yaudarar amfani da kudade wadda yake zargin wadansu jam’iyyu domin sayen kuru’un al’umma musamman talakawa a kakar zabe mai zuwa.
Daga karshe ya sha alwashin bunkasa jin dadin al’umma ta hanyar bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga mata da matasa matukar al’ummar jihar suka ara masa wannan dama ta darewa kujerar gwamnan jihar ta Jigawa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: