Connect with us

LABARAI

Jigawa Ta Yi Rajistar Yara 722,000 Don Ciyar Da Su A Makaranta

Published

on

Gwamnatin jihar jigawa ta bayyana cewar ‘yan makarantun firamare dada aji hud zuwa shidda wadanda suka kai 722,000, za su amfana da tsarin gwamnati na ciyar da ‘yan makaranta.
Mataimakin gwamnan jihar Ibrahim Hassan shine ya bayyana haka lokacin da yake jawabi akan ala’amarin wayar da kan wadanda suke da ruwa da kuma tsaki, ranar Talata a garin Kaugama.
Mataimakin gwamnan Ibrahim Hassan har ila yau ya bayyana cewar za kuma a dauki masu girka abincin wadanda suka kai, 7,100, saboda shi tsarin na ciyara da ‘yan makarantar.
Ya ce, shi tsarinkasance kamar tsarin da gwamnatin tarayya take yi ne, wanda ita tana yi ma ‘yan makarantar firamare daga aji daya zuwa aji uku.
Mataimakin gwamnan ya bayyana cewar su wadanda za su rika dafa abincin an zabe sune, bayan an dauki wasu matakai da kuma al’amarin nuna cancanta, wannan kuma bai danganci ko wacce jam’iyyar siyasa suke ba goyon baya ba.
Hassan ya yi kira dasu wadanda za su rika dafa abincin da cewar su nuna halin gaskiya da ,uma rikon amana, na ganin koda wanne lokaci sun shirya abinci mai tsafta,
Shima da yake fadar ta albarkacin bakin shi babban jami’in jin dadain al’umma ta zuba jari na jihar Alhaji Bala Chamo, ya kara tunantar da su matan cewar, shi tsarin ya taimaka wa m ata da yawa. a wuraren da za su yi aikin,
Shi yasa ma ya yi kira gasu wadanda za su rika dafawa ‘yan nmakarantar abincin , dasu rungumi tsarin taimaka masu da aka yi, ta wajen maida hankali ga aikin su da kuma lura sosai.
Ya jinjina ma gwamnatocin tarayya da kuma na jihohi saboda ci gaba da yin tsarin, wanda, a cewar shi zai kara hazakar su ‘yan makarantar.
A tashi gudunmawar Shugaban karamar Hukumar Kaugama Alhaji Ahmed Yahaya ya dauki alkawarin cewar zai hada kai da gwamnatocin tarayya da kuma na jihohi, saboda kara samun lagwadar damukuradiyya a karamar Hukumar.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya bada rahoton cewar ranar 29 ga watan Nuwamba na shekarar 2017, gwamnatin tarayya ta kaddamar da tsarin na ciyar da ‘yasn makarantar firamare aji daya zuwa uku, wadanda suka kai 726,033 najihar Jigawa.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya bada rahoton cewar an kaddamar da shi tsarin ne a makarantar Firamare ta Nuhu Muhammad Sunusi dake Dutse.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: