Connect with us

MANYAN LABARAI

Kaddamar Da Kamfen Din Atiku: El-Rufai Da Shehu Sani Sun Yi Musayar Kalamai

Published

on

  • Daga Nijar PDP Ta Dauko Hayar Jama’a —Gwamna el-Rufai
  • Kana Iya Hayar Na Ku Jama’an Daga Sudan —Sanata Shehu Sani

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir el-Rufai, ya yi zargin cewa, jama’ar da suka halarci gangamin taron yakin neman zaben jam’iyyar PDP da aka yi a garin Sakkwato ranar Litinin sojan gona ne da aka yi hayarsu daga Jamhoriyyar Nijar.
El-Rufai, ya yi wannan zargin ne a taron kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa na jam’iyyar APC na jihar Kaduna, ya ce, jami’iyyar PDP ba ta da wani abun da ta tanadar wa Nijeriya na ci gaba.
Ya ci gaba da kwatanta taron kaddamar da jam’iyyar PDP da aka yi a Sakkwato da taro ne na barayi.
El-Rufai ya kuma kara da cewa, “Barayi sun yi gungu sun kuma yi taron dangi a kan shugaba Muhammadu Buhari, jiya sun yi taro a Sakkwato inda suka yi hayan jama’a daga jamhoriyyar Nijar don su nuna wa jama’a kamar suna da mutane, saboda sun lura mutane cewa, mutane Sakkwato ba zasu halarci taron ba.

“Saboda haka, in mun shirya kaddamar da taron yakin neman zaben shugaban Kasa Muhammadu Buhari a garin Kaduna, mutane za su ga abin da ake kira taron jama’a, ba kamar taron da aka hada ‘yan kasar Nijar ba da sunan ‘yan Nijeriya.”
Gwaman ya na jawabi ne a yayin kaddamar da kwamitin mutum 69 na yakin neman zaben jam’iyyar APC a jihar Kaduna, ya kuma kara da cewa, zaben shekarar 2019, zabe ne a tsakanin shugabanin masu kishin kasa da kuma barayin da suka tafi Abuja suka sace kudaden jama’a.
Ya kuma kara da cewa, gwamnatin jam’iyyar APC sun shirya tsarin tafiyar da gwamnati mai tafiya da mutane, “Gwamnatinmu ta samar da ayyukan yi ga dukkan jama’ar kasa tun da ta hau karagar mulki a shekarar 2015.”
“Tun shirya karfafa mutanen kasar nan ta hanyar gabatar da jama’a a gaba a dukkan shirye shiryenmu.
“Muna kara inganta rayuwar jama’a, ta hanyar sake tsara harkokin gwamnati ta yadda za mu bayar da karfi a bangaren bukasa rayuwar jama’a gaba daya.”
Gwamnan ya kuma ce, gwamnatin APC ta na aiki gyara barnar da jam’iyyar PDP ta yi ne a tsawon shekara 16 da ta yi tana mulki.
Ya kuma kara da cewa, “Babban aikin da yake a gaban mu a shekarar 2019 shi ne samar da cikakken ci gaba ga jama’armu, ta hanyar daukaka darajar rayuwarsu. Ba za mu yarda mulki ya sake komawa hannun mutane marasa tunani ba kuma barayi.
“Babu abin da PDP za su iya kawo wa mutanen jihar Kaduna, babu abin da za su iya kawo mutanen Nijeriya, a tsawaon shekara 16 da suka yi suna mulki, makarantu fiye da 4,250 sun tabarbare da yawa basu da bayi da winduna da kofofi, duk sun lalace.”
Sanata Sani Shehu, Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, ya shawar ci jam’iyyar APC su kwaso hayar nasu jama’ar daga kasar Sudan.
Shehu ya yi wannna bayanin ne a martaninsa ga Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, inda ya ce, wadanda suka halarci taron kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar PDP da aka gudanar a garin Skwatto an yi hayan su ne daga kasar Nijar.
Ya mayar da martanin ne ta shafinsa na Twitter, in da ya kara da cewa, “Sun yi hayan nasu jama’a daga kasar Nijar saboda kusanci, ku kuma ku yi naku hayan jama’a daga kasar Sudan saboda ‘yan uwantaka.”
Ranar Talata ne, El-Rufai ya kaddamar da kwamiti mai kunshe da mutum 69 da za su jagoranci yakin neman zaben jam’iyyar APC a jihar Kaduna. “Barayi sun yi gangami a kan Shugaba Muhammadu Buhari. Jiya suka yi hayan sojan gona daga kasar Nijar saboda mutanen Sakkwato sun ki halatar taron.
“Saboda haka in mu zo kaddamar da yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari a Kaduna, muna bukatar duk duniya su fito su gani, ba sojan gona bane daga jumhoriyyar Nija.”
Shehu da El-Rufai dai sun dade ba sa ga maciji a tsakaninsu, saboda matsalar siyasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!