Connect with us

WASANNI

Karanta Yadda Dan Wasa Messi Ya Ji Kunya A Wannan Shekarar

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid kuma dan asalin kasar Croatia, wato Luka Modric ya lashe kyautar Ballon d”Or ta 2018.
Wannan shi ake cewa komai nisan dare gari zai waye domin kuwa Modric ya kawo karshen mulkin mallaka da raba daidai da kuma bani na baka da Cristiano Robaldo da Leonel Messi suke yiwa wannan kyauta.
Modric ya lashe kyautar ne da maki 753, kuma ya sami wannan maki ne ta hanyar daukan gasar zakarun turai da ya taimakawa kungiyar sa ta Real Madrid ta dauka har sau 3 a jere sannan kuma ya jagoranci kasar sa har taje wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka yi a kasar Russia inda Croatia ta karkare a matsayi na 2.
Rabon da wani dan wasa ya lashe wannan kyauta idan ba Messi ko Ronaldo ba tun 2007 da dan wasa Kaka ya lashe a kungiyar A.C Milan, sai yanzu da Modric ya ta ka musu birki.
Ga jerin wasu ‘yan wasan da suka fafata a gasar lashe wannan kyauta da makin da suka samu.
Modric ya sami maki 753.
Cristiano Rinaldo ya sami maki 476.
Griezmann ya sami maki 414.
Mbappé ya sami maki 347.
Messi ya sami maki 280.
Mohammed Salah ya sami maki 188.
7.Raphael Jabier Barane ya sami maki 121.
Eden Harazard ya sami maki 119.
Kevin De Bruyne ya sami maki 29.
Harry Kane ya sami maki 25.
N’Golo kanté ya sami maki 24.
Neymar ya sami maki 19.
Suarez ya sami maki 17.
Courtois ya sami maki 12.
Pogba ya sami maki 9.
Sergio Aguero ya sami maki 7.
Gareth Bale da Karim Benzema kowa ya sami maki 6.
19.Firmino da Rakitic da Ramos kowa ya sami maki 4.
Yanzu haka ta tabbata a wannan shekarar da muke ciki Luka Modric ya lashe kyaututtuka da dama, amma manya guda biyu sune kyautar Ballon d”Or da kuma zakaran gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!