Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Kotu Ta Umurci Lalata Sunduki 14 Na Tramadol

Published

on

A ranar Talata ne babbar kotun jihar Legas ta bayar da umurnin lalata sunduki 14 na tramado wanda hukumar kwastam ta kama daga hannun masu fasa kwauri. Alkali mai shari’a Saliu Saliu ya bayar da wannan umurni ne, biyo bayan kiran da lauya mai gabatar da kara ya yi.
Lauyan hukumar kwastam Mista Bisi Ogunlowo ya bayyana kotu cewa, hukumar kwastam ta kama kwayar ne tsakanin watan Fabriru da kuma watan Satumbar cikin wannan shekara a bakin tekun Apapa da ke Legas. Ya kara da cewa, an kama sundukin 14 na kwayan Tramadol wanda aka shigowa da shi daga hannun masu fasa kwauri. Ya ci gaba da cewa, tun lokacin da suka cafke wannan sundukin, babu wani da ya yi ikirarin cewa na shi ne. Ogunlowo ya bayyana cewa, hukumar kwastam ba ta samu wata kara ba game da wannan lamari. Domin haka yana kira ga alkali mai shari’a Saidu ya baiwa hukumar kwastam dama a kan ta lalata wannan kwaya, domin ya saba wa sashi na 167 da kuma sashi na 169 (1) mai lamba ta 3 C.45 na dokar hukumar kwastam ta Nijeriya na shekarar 2004.
Alkali ya amince da rokon sa inda ya bayyana cewa, “Na saurari lauya mai gabatar da kara sannan na amince da bukatar sa.”
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: