Connect with us

WASANNI

Liverpool Da Arsenal Suna Fafatawa Akan Siyan Rabiot

Published

on

A yunkurin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool dake kasar Ingila na ganin ta rike kambunta na cigaba da zama cikin sahun gaba a nahiyar Turai, kungiyar na kara matsa kaimi domin daukar dan wasan PSG Adrian Rabiot.
Liverpool dai ta kai wasan karshe na gasar zakarun nahiyar Turai a kakar wasan data gabata amma ta yi rashin nasara a hannun kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid daci 3-1a wasan karshen da suka buga a kasar Ukraine .
Ganin kokarin da ta yi ne ya sanya ta shiga kasuwa ta sake siyan dan wasan gaba Shakiri da Fabinho da kuma Kaita sai ga shi kuma tana sake matsa lambar daukar wani zakakurin dan wasan na tsakiya.
Rabiot dai har ya zuwa yanzu bai sake rattaba wata sabuwar yarjejeniya da kungiyarsa ta PSG ba wanda hakan zaisa ya tafi a matsayin kyauta da zarar kakar wasanni ta bana ta kare, matukar basu sayar da shi a watan Janairun shekara mai kamawa ba ko kuma ya tsawaita kwantaragin nasa ba.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City da AC Millan da Inter Millan dai duk sunyi zawarcin dan wasan dan asalin kasar Faransa sai dai kungiyarsa taki siyar da dan wasan tun a kwanakin baya.
Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenak, Unai Emery ma yana zawarcin dan wasan wanda sunyi aiki tare a kungiyar kwallon kafa ta PSG a lokacin da Emery din yana koyar da PSG din.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: