Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Magidanci Ya Kashe Kansa Ta Hanyar Fada Wa Jirgin Kasa

Published

on

‘Yan sanda a Abuja suna kokarin gano wani mutum wanda ya mutu a tashar jirgin kasa da ke Phikwore cikin garin Kubwa ranar Litinin.‘Yan sanda sun dangata lamarin da cewa, mutumin ya kashe kansa ne lokacin da ya yi tsalle ya fada titin jirgin sa’ilin da jirgi ke wuce wa. Jirgin ya yi gunduwa-guduwa da mutumin, inda aka tattara namansa aka ijiye a dakin ijiye gawargaki da ke babban asibitin Kubwa.
Kakakin rundunar ‘yan sanda reshan Kubwa CSP Surajdeen Ayobami ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Talata, ya bayyana cbewa, an samu takardar wasiyya a aljihun mamacin. Ya kara da cewa, “Mun samu takarda a aljihunsa wanda yake yi wa Nijeriya da kuma ‘yan Nijeriya addu’a, ya kuma roki iyalansa a kan su yafe masa dukkan laifin da ya yi musu. Akwai lambar waya a cikin takardar, amma ‘yan sanda basu samu wayar ba. “Mun ta kiran lambar wayan, amma ba ta shiga ba, mun tabbatar da cewa, za mu iya gane mamacin idan da mun samu lambar wayan da ke cikin takardan.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!