Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Mutum Daya Ya Mutu A Harin ‘Yan Bindiga A Garin Esa-Oke

Published

on

A ranar Talata ne wadansu ‘yan bindiga sun farmaki garin Esa-Oke da ke karamar hukumar Obokun cikin jihar Osun. Zuwa lokacin da ake hada wannan labara, an bayyana cewa, har yanzu ba a gama gano sauran mazauna yankin wadanda suka shiga daji a guje ba. An dai bayyana cewa, farmakin ya fara ne daga yankin Onireke, sannan ya watsu zuwa sauran yankunan. Wani mutum mai suna Olaniyi wanda yake aiki a kwalejin kimiya ta jihar Osun da ke Esa-Oke, ya mutu sakamakon wannan farmakin. Wani ma’aikacin kwalejin ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a wayar tarho. “Ba a samu hada sunayen wadanda suka gudu zuwa cikin daji domin gujewa harbi daga farmakin,” inji shi.
An bayyana cewa, maharan sun yi garkuwa da wadansu mazauna yankin.
Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa, maharan sun harbi wani dan sanda guda daya.
Wani mazaunin yankin mai suna Oladepo ya bayyana wa manema labarai a waya cewa, har yanzu ba a gano maharan ba. Ya kara da cewa, “Har yanzu ba a bayyana maharan ba da kuma manufar su. An kashe wani ma’aikacin kwalejin kimiya, yayin da wasu mutanen suka bace. Lokacin da lamarin ya auku, wasu mazauna yankin sun shiga daji da gudu, kuma har yanzu ba a gano saura daga cikin su ba. An harbi wani dan sanda, amma yana nan a raye.”
A bayanin darantan watsa labarai na kwalejin kimiya ta jihar Osun, Prince Wale Oyekanmi wanda aka karanta kamar haka; “An samu farmaki a kan titin Esa-Oke da yamma bayan an tashi daga aiki, sunayen ma’aikatan kwalejin kimiya ta jihar Osun wadanda aka yi garkuwa da su a daji sun hada da; Mista Olaleye Olalekan na sashin kasuwanci, Adeyeoluwa Bankole shugaban sashin karatun injiniya, Dakta Jesuola Ajibola daraktan kwalejin, Adenreti Chukwu sakataran sashin karatun injiniya, Olaniyi Emmanuel Temitope wanda yake aiki a ofishin rajista shi ya mutum nan take, sai kuma Rachael Onyinocha Akinboboye wanda yake aiki a bankin Microfinance banka. Wadannan su ne sunayen da muka iya ganewa wanda suka bace.”
Wakilinmu bai sami kakakin rundunan ‘yan sanda Folasade Odoro a waya ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!