Connect with us

SIYASA

Ta Hanyar Samawa Matasa Aiki Ne Za a Gane An Samu Canji A Tarauni –Hafiz Kawu

Published

on

Babban Hadimi ga Mataimakin shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbanjo, Kwamared Honorabul Hafizu Kawu Dan Takarar zam Dan Majalisar wakilai a Karamar Hukumar Tarauni a Jam’iyyar APC ya bayyana cewa abinda zai ba mahimmanci shi ne samawa Matasa aikin yi a Karamar Hukumar Tarauni da zarar ya zama dan Majalisar wakilai ta Tarayya da ke Abuja wanda ta haka ne za a gane cewa yanzu ansamu sauyi ko canji a wakilcin Karamar Hukumar Tarauni wanda ake kokawa na rashin ganin wakilinsu a mazabu 10 na Karamar Hukumar Tarauni.
Kwamared Hafiz Kawu wanda ya bayyana haka a wajan taron Makarantar Islamiyya da ke unguwar Sallari Babban Giji ya ce dole ne wakilini Al’umma dole ne Jama’arsa su rika ganin sa domin Jama’a yake ma hidima ba sune za su rika masa hidima ba dan haka ya yi alwashin taimakawa al’umma ta hanyar ziyartar su ko yaushe ya kuma ba Makarantar mai suna Fatahurrahaman zunzurutun kudi har Naira 20,000 in da kuma ya yi alwashin ciyar da Karamar Hukumar Tarauni gaba a wannan wakilci da yake nema ta hanyar Tallafawa Matasa koyar da Sana’o’i samar da aiki da kuma horar da Sana’oi ta yadda Al’ummar Tarauni za su amfana Mazan su da Matan su.
Shi kuwa shugaban Makarantar Adam Abdullahi ya bayyana cewa Dalibai 58 ne kuma suna kokari wajan ganin sun cusama Dalibansu kishin Al’umma, da kishin Kasa da san zaman lafiya a tsakanin Al’umma mabanbantan ra’ayin Siyasa da fahimtar Addini kasancewar Addini abu ne da ba cuta ba cutarwa a cikin sa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!