Connect with us

LABARAI

Tarayyar Turai Za Ta Dage Wa Nijeriya Haramcin Shiga da Wake A Shekarar 2019

Published

on

Ma’aikatar gona da raya karkara ta bayyana cewar dakatarwar da kungiyar Tarayyar Turai tayi ma kasar Nijeriya, dangane da sayar da busasshen , busasshen kifi dasauran wasu kayayyakin gona nan bada dadewa bane za a dage shi takunkumin.
Misis Heather Akanni wadda ita mai bayar da shawara ce akan nagartar kayayyakin amfanin gona ta Ministan aikin gona Mista Audu Ogbeh, ita ce wadda ta bayar da wannan tabbacin, a wata hirar da ta yi da Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ranar Talata a Legas.
Akanni ta yi shi wannan bayanin ne lokacin da aka kaddamar da tsarin ne akan yadda ake gyara amfanin gona, da kuma yadda za a bunkasa rayuwar al’umma, wanda wani tsari ne na Bankin duniya.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya bada rahoton cewar dakatarwar da kungiyar Tarayyar Turai tayi ma kasar Nijeriya, daga sayar da wasu kayayyakin amfanin gonarta, a shekarar 2015 bayan da aka gano cewar, suna da guba, wannan kuma ya faru ne bayan abincin da aka saya daga Nijeriya. Akanni ta bayyana cewar ita ma’aikatar ta dauki matakai wadanda za su sa ita kungiyar Trayyar Turai ta canza matakin data dauka a shekarar 2019.
Ta kara bayyana cewar yadda aka kara inganta nagartar kayayyakin da ake amfani dasu a ghida, da kuma kai su zuwa kasashen waje, wannan al’amarin ya zama dole, saboda al’amarin aikin gona ya fara zama wani babban abin da Nijeriya zata dogara da shi wajen samun kudaden shiga.
Kamar dai yadda mataimakiyar Ministan ta kara jaddadawa shi kafa bangaren lura da inganci da kuma lura da kayayyakin amfanin gona, wanda gwamnatin tarayya ta kafa. an yi al’amarin saboda a tabbatar da a rika samar da kayayyakin amfanin gona masu inganci, domin hakan ne zai su kayayyakin su yi farin jini a kasashen waje.
“Daga cikin shi al’amarin wani kwamitin minita ne na cikin gida wanda kuma bai wuce yadda ya dace a yi shi al’amarin ba, saboda ya duba sosai ga bangaren da ya shafi wannan, na tabbtar da cewar an samu dage shi takunkumin.
“Shi tsarin niyyar kaw ala’amarin na kawo karsshen takunkumin wanda kuma majalisar dinkin duniya tana goyon bayan al’amarin, da kuma ci gaban masana’antu, an bullo da tsarin ne saboda asamar da ingantattun kayayyakin amfanin gona, wanda kuma ana iya tunawa da al’amarin Wake a matsayin misali.
“Muna da wani kyakkyawan tsari wanda muka yi dangane da fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, wanda kuma an yi abin ne cikin hikima, saboda, kuma zata kasance sanadiyar dage mana takunkumin da aka sa mana a sanadiyar wake.
Ta ci gaba da bayanin cewar, ”muddin da aka yi sa a aka cire shi takunkumin wanda ya shafi wake, sai abin kuma a hankali ya shafi wasu kayayyakin, muna yin duk abubuwan da suka kamata saboda a samu ci gaban abubuwan da za su kawo kudaden shiga ma kasar Nijeriya.”
Sai dai kuma Akanni ta nuna rashin jin dadinta akan rashin sani ko kuma jahilci na wasu manoman Nijeriya, wadanda su basu gane abin da ake nufi da muhimmancin ingantattun kayayyakin amfanin gona da kuma kulawa dasu, ta kuma cewar tsarin APPEALS zai taimaka wajen dinke duk wata barakar da ake da ita.
Da kuma rake bayani akan faifan bidiyo wanda yake nuna wani dankasuwa wamda yake sayar da Wake, yana mafani da sniper (a pesticide) saboda ya kare ma shi Waken shi, a matsayin wani abin da bai dace ba ne saboda hakan ya nuna cewar ‘yan Nijeriya suna cin Wake wanda yake da guba.
Mai bada shawarar akan fasaha ta bayyana cewar “Mista Audu Ogbeh ya gaji shi al’amarin takunkumin da kungiyar tarayyar Turai ta sa ma Nijeiya shekarar 2015, muna juma sa ran za a dage shi takunkumin cikin watanni biyar masu zuwa, wanda abin zai kai shekarar 2019,
“Yayin da muke yin hakan sai muka ga wani mutum yana amfani da sniper wai saboda ya kare waken shi daga lalacewa, gare mu wannan ya nuna ke nan muna cin guba, koda yake dai muna amfani ne da wasu hanyoyi wajenn ilmantar da manoma yadda zau kare wakens daga baci, mu gare mu hakan ya nun aba barci muke yi ba, saboda muna bin duk hanyoyin da suka kamata domin wayar da kan manoma yadda za su kula da ajiye waken su ba sai ya baci ba. t
“ Yawancin lokutta manoma wajen duba lafiyar waken mu suna yin wadansu al’amura saboda rashin sanim wannan shi yasa muka nemi hadin kai na Hukumomin kula da abinci dam kuma ingancin magani ta kasa (NAFDAC) da kuma ta kula da ingancin kayayyaki ta kasa (SON).
“ Haka nan ma Hukumar kula da kuma sa ido a kayayyakin da ake kaiwa kasashen waje, (NEPC), sai kuma Hukumar hana fasa kwauri (NCS) sai kuma Hukumar kulawa da tasoshin jiragen ruwa (NPA) ga kuma Hukumar kulawa da ingancin kayayyakin amfanin gona FPIS kamar dai yadda ta kara jaddadawa.
Daga karshe Akanni ya bayyana ba wasu fasahohin zamani wadanda za a yi amfani da su wajen gane idan wake yana wani sinadarin da zai cutar da masu amfani da shi a kasuwa.“Shi ya sa yana da kyau su masu amfani da waken su dafa shi sosai kafin su ci shi.’’.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!