Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Wani Saurayi Ya Damfari Budurwarsa Naira Miliyan 5

Published

on

An garfanar da wani dillalin gidaje mai suna Gbemini Babajide dan shekara 35 a gaban kotun Ikeja, bisa damfarar badurwarsa naira miliyan 5. Wanda ake tuhumar yana zauna ne a kan titin mai lamba 10 Bolarinwa cikin Kajola da ke Ibadan ta jihar Oyo, ana tuhumar sa da laifuka guda biyu wadanda suka hada da na damfar da kuma na sata. An dai bayyana cewa, wanda ake tuhuma ya amshi naira miliyan 5 daga hannun budurwarsa mai suna Oluwaseun Giwa, domin ya taimaka mata wajen bunkasa kasuwancin ta. A ciwar lauya mai gabatar da kara, Michael Unah ya bayyana cewa, wanda ake tuhama ya aikata laifin ne a tsakanin shekarar 2014 da kuma shekarar 2016 a garin Surulere cikin jihar Legas. Unah ya kara da cewa, budurwar ta tura masa naira miliyan 5 a cikin asusun shi, wanda take so ta bude babban kanti da su,a kan ya ijiye mata. Lauyan ya ci gaba da cewa, “Budurwar ta bashi wannan naira miliyan 5 ne ya kula mata da su, domin ta san akwai kyakkyawan alaka a tsanin su. “Wanda ake tuhuma ya yi amfani da wannan kudi wajen bukatar kansa ba tare da ta sani ba. “Duk wani kokari da ya yi domin ya maida wannan kudi ya ci tura, idan ta tambaye shi a kan kudin sai ya yi bushi tare da yi mata barazana.”
Unah ya ce, laifin ya saba wa sashi na 287, 314 da kuma sashi na 411 tsarin mulkin jihar Legas ta shekarar 2015 (wanda a kai mata bita). A cewarsa, sashi na 287 ya bayar da umurnin a hutanta duk wanda aka same shi ya yi sata, to za a daure shi na tsawan shekaru bakwai a gidan yari, yayin da sashi na 314 ya umarci a daure duk wani wanda ya yi damfara na tsawan shekara 15 a gidan yari.
Wanda ake tuhuma ya musanta zargin da ake masa.
Alkali mai shari’a Mista A. A. Fashola ya bayar da belin wanda ake tuhuma a kan kudi naira 250,000 tare da masu tsaya masa mutum biyu. Fashola ya bayyana cewa, wadanda za su tsaya masa ya kasan ce suna aikin, sannan suna da takardar biyan kudin haraji na tsawon shekaru uku, kuma sai kotu ta tabbatar da wajen da suke zama. Ya kara da cewa, masu tsaya masan sai suna da gida kusa da kotun. Alkali mai shari’a ya dage sauraran wannan kara har sai ranar 30 ga watan Junairu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!