Connect with us

WASANNI

Welbeck Zai Bar Arsenal A Karshen Kaka

Published

on

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal baza ta sake karawa dan wasa Danny Welbeck sabon kwantaragi ba saboda a cewarta bata bukatar sad a salon wasansa yanzu.
Hakan yasa ake ganin abu ne mai wahala dan wasan ya sake bugawa kungiyar wasa nan gaba bayan da daman yana jinya kuma zai dauki tsawon lokaci bai dawo ba inda ake zaton za’ayi masa tiyata har sau biyu.
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dai ta siyi Welbeck ne daga kungiyar Manchester United a shekara ta 2014 akan kudi fam miliyan 15 a lokacin tsohon kociyan kungiyar Mista Arsene Wenger.
Ana tunanin Welbeck zaibi sahun dan wasa Ramsey wajen barin kungiyar ta Arsenal bayan da shima kungiyar tace baza ta kara masa sabuwar yarjejeniya ba sakamakon kociyan kungiyar bayason yin anfani dashi.
A kwanakin baya ne dai dan wasa Welbeck yaji ciwo a lokacin da yake bugawa kungiyar wasa a wasan gasar Europa ta nahiyar turai kuma nan gaba ana tunanin zai dauki wata da watanni yana jiyya.
Kungiyoyi da dama dai a kwanakin baya sun nemi dan wasan da suka hada da Bournemouth da Cardiff da kungiyar kwallon kafa ta AC Millan dake kasar Italiya sannan kuma kungiyar Lyon ta kasar Faransa ma ta nemi siyansa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!