Connect with us

MANYAN LABARAI

Yajin Aiki: An Tashi Baram-baram Tsakanin ASUU Da Gwamnati

Published

on

Wani taron sasantawan da aka kara yi a tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin kungiyar malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU), a daren ranar Talata, ya watse ba tare da cimma wata matsaya ba.
An yi taron ne a Ma’aikatar Ilimi ta tarayya domin lalubo maslaha ta karshe ta kawo karshen yajin aikin da malaman Jami’o’in suke yi.
Akalla an yi wasu tarukan biyu kafin na ranar Talata din tun bayan soma yajin aikin malaman Jami’o’in.
Tun a ranar 4 ga watan Nuwamba ne kungiyar ta ASUU ta shiga yajin aikin shiga aji, a kan abin da ta kira da rikon sakainar kashin da gwamnati ke yi wa Jami’o’in kasar ta hanyar rashin ba su kudaden da ya kamata, da kuma kin cika yarjeniyoyin da gwamnati ta cimma da malaman a baya.
Da yake magana da manema labarai bayan tashi daga taron na ranar Talatan, Shugaban kungiyar malaman Jami’o’in, Biodun Ogunyemi, cewa ya yi dukkanin sassan ba su iya kaiwa ga wata matsaya ba.
“A halin yanzun dai mun fara tattaunawa, amma ba mu cimma matsaya ba. In kuma mun sami wani karin bayani za mu sanar da ku,” in ji shi.
A cewar sa, kwanan nan ne za su sake yin wani taron domin ci gaba da tattaunawa.
Wakilan sashen gwamnati a wajen tattaunawar sun hada da, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, babban Sakatare a Ma’aikatar ta Ilimi, Sunny Echono, wakili daga hukumar kula da Jami’o’i ta kasa, da kuma wakili daga hukumar kula da albashi da alawus-alawus na ma’aikata.
Hakanan kuma, shugaban kungiyar dalibai ta kasa, Danielson Akpan, ya yi kira ga dukkanin sassan biyu da su hanzarta kaiwa ga wata matsaya, ko dalibai sa samu komawa ajujuwan su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!